Wednesday 30 December 2015

"NIMA MACECE" Episode 2 30th Dec 2015



Bude idonta keda wuya taganta awani daki. Wanda tunda uwarta ta haifeta bata taba ganiba. Dakin bakomai sai kyankasaye da beraye a razane tafara ihu. Wanda yajanyo hankalinsu ogansu bakinkirin kato basamude fuskanshi a tamuke ya kalleta ke bamuson rakin tsiya munkiraki nanne don cimma burin mu agun mahaifinki bawai mu ajiye kaman hotoba.
 Ta kalleshi ta zuba mar harara kai matsiyacin inane?. Yazaayi ka kawoni dakin bera ka ajiyeni da darajana da komi? Wani dariya yasake wanda saidata firgita yace ba hutu kika zoba kinzo bautane. Gashinta yacafko yajawota ihu takeyi ganin zata cika musu kunne yasa yadauko seletape manyannan yatoshe mata baki.

Fusganta yake dakarfi kaman wanda yake fusgan buhun shinkafa. Look anmata dont mess up with me inbahaka ba zanmiki tsiya. Tayi tsit don ta razana sosai da bayin Allahn. Ta kumshe jikinta kaman mage wani daki ya cusata. Sannan yadanna kira tare dasawa a handsfree. Acan aka dauka tare da sallama. Muryan mahaifinta taji cikin tsananin kidima zatayi magana yanausheta wanda yasa tabuga kanta da bango.yace alhaji batare da dogon bayani zamubaka sharudda kuma dole kabi don ceto rayiwar yarka. Miliyan 600 mukeso. Cikin rashin damuwa alhaji yace you are not serious aina zakuga yar tawa? Mutumin wanda gaba daya basant ta tsorata dashi ganinshi take kaman malaikan mutuwa yabata wayan sannan yafinciko gashinta ihu tayi tare dacewa daddyy wayyo daddy zasu kasheni. Alhaji ibrahim cikin tashin hankali yace basant?. Kina ina?. Meya sameki?. Batasamu daman amsa mishiba alokacin basamuden ya kara a kunnensa sannan yace zaka yi magana da ita idan kashirya biyan kudin. Alhaji yace badamuwa aina zankawo muku? mutumin yayi murmushi gaskiya harka da irinku da dadi. Kasan voice of nigeria.?. Yace ae!. A cikin gurin sign board zaka mike har cikin jejin zakaga canopy agun ka ajiye kudin agun. Sannan idan kasanar da hukuma tamkar kace mu kashe maka yarka ne. So akiyaye doka a zauna lafiya .Alhaji iby yace anyi angama .
Basamude sunanda basant tasamasa a zuciyanta ya kalleta sannan yace babanki nasonki yarinya!. Ki zauna anan har kudinmu yashigo hannu. Kuka mai tsima rai takeyi . Gani take bazata fita agunba. Alhaji iby cikin kidima yafita bai nufi ko inaba sai banki yacire kudin sannan yanufi inda akamasa kwatance ya ajiye kudin sannan yakira. Inda basamude yadauka alhaji iby yasanar masa dacewa ya ajiye kudin. Yace to kaje zakaga yarka a gida. Atake ya aika aka dauko kudin shida abokan aikinshi sunzauna sunga kudin cif yacika. Ga basant a agabansu tace tunda anbaku kudin kutaimaka don Allah kumayar dani gun mahaifina, Basamuden ya kalleta sannan yace yarinya dazamu mayar dake anma munyi tunani mai kyau bazamu mayar dakeba kicire ranki da gida sannan yanzu kinzama medium tsakaninmu da dad dinki kudi zamuyi yadda yakamata. Cikin kidima tace kuyi hakuri don Allah duk abinda kukeso zanbaku kubarni natafi . Dariya suka rinkayi wanda itakuwa kuka takeyi. Dayan yace oga tunda fauza takimu mezai hana mu kama wannan? Basamuden yakalli basant sannan yace anma fa kayi tunani sosai. Yace kafin nan ku gyara wancan dakin zamuji dadin harkan dakyau. Suka mike suka fice. Yayinda ya matso kusa da basant. Hannunsa yadaura akanta yana shafata ahankali. Bugeshi tayi dakarfi yayi dariya sannan yace kigama gwallinki you are now my new wife.
Wani irim firgita tayi wanda zuciyanta saida ya buga nashiga uku don Allah kayi hakuri. Yace inafa!!! **alhaji iby yajira baiga basant ba donhaka yakira yaji dalili. Tunda nabaku kudinku kusake min ya. Firgita alhajin yayi alokacin da basamuden yake sanar dashi burinsa narike basant har abada. Sannan yace kar kayi garajen tinanin nemanta tazama namu har abada. Zufa da gumi ne yaketo ma alhaji duk da sanyin ac daya ratsa dakin adda ne tashigo tare dacewa nifa yau lafiya tunda basant tabika office shiru nakeji numbanta kuma nakira bata dauka. Alhaji cikin kuka wiwi yasanar da adda suma tayi tashin hankali atake suka nufi asibiti yashiga sanar da yanuwa da abokan arziki. Nanfa hankalin jamaa yatashi. Labari yabaza garin nigeria cewa ansace ya kwaya daya tilo agun alhaji fawu.
 Kash munzo karshen kashi na biyu, a biyo mu sati mai zuwa domin cigaba. Add 08066680993 for more updates and other stories on whatsapp. Feel free to comment below thanks.

No comments:

Post a Comment