Wednesday 27 January 2016

Nima Macece Episode 6 27th January 2015


If you miss the previous episode click Here

Gida yanufa da ita suna tadi tace baranje nayi wanka. Yace ban wayanki nayi game tace kaidai kaman yaro. Yace temple run bayaro ba babba. Tashiga kenan adda tafito takalleshi ahmadu ana kan aiki ko. Yayi murmushin jin dadi yace sosaima ai yanxu nasamu hanyan dazai kaini har gun basant ina bi a hankali ne tace to Allah nuna mana Allah saka da alheri. Yadauki wayan yayi text wa numban dayake zargi. Where are you?. Cikin mintuna kadan aka turo Guest house, inkina tahowa kisayawa basant pizza! Yamayar da o.k. tananan kalao ko?. Akadawo da sosaima aikinmu nakyau ai. Wani irin dadi ahmed yaji yagoge text din yabar inkina tahowa ki sayowa basant pizza. Saboda tagani kartace tamanta suyi zargi. Bayan fitowarta sundanyi tadi yace zaishiga daga ciki. Bataso hakaba don a yanda take jinsa ba abunda bazata iya masaba. Sukayi sallama

**Basant na zaune asiri duk yacita hatta ibada tamanta ya akeyi. . Tace tasha shine aikin. Suci soyayyansu da basamude. Ahmed ne zaune a kujera saiga ruky tafito da dan sauri good morning dear. Yace ina zaki haka?. Cikin sauri tace zankai aikane wani gu. Yace safe journey. Fitanta keda wuya yamike bayan fitarta da motanta yadauki motan abokinsa wanda batasan da motarba. Yabi sawunta pizza taje tasiyo duk yana biye da ita kafin tawuce, da dabara yakebinta har ta isa inda yake zargin anan basanta take. . Shiganta keda wuya yaja motansa yakoma.
*Tunani yake sosai yanda zai bullowa lamarin yafada wa yansanda kokuma yaje shikadai?. Gaskiya gwara yaje shikadai Saida yayi sati yana monitoring din ruky da basamude. Yalura da lokutan da basamude yakefita da dawowa. Yalura cewa su uku ne agidan anma sauran yarane. Saikuma ruky. Saikuma wata mace wacce bai ganetaba (basant kenan). Yasissiyo kayan aikinsa, Randa yashirya musu tabargaza ranan yatashi da sassafe bakin kaya yaci. Kaman yanda yalura duk wanda suke gidan suke sawa. Batarda kamanni yayi yasaje dasu. Dafarko yanufi bakin gate din maigadin yaleko . Ganin kayan jikinsa yasa yabude tareda masa barka. Yace suna ciki?. Maigadin yace a a . Haj. Ce kawai.Tabaya yanufa window biyu yagani yaleka daya baiga kowa ba yaleka dayan yaga wata azaune. Sanin ba mutane agidan yashiga kallonta yake sosai. Yace ina basant bata tsorataba kodai dontaga shiganshine. Tace ni ce. Meyene. Yace zomuje basamude ne ya aikon. Tatashi tasaka hijabinta yariko hannunta sukafito yakalli maigadin yace bari muje mudawo. Tusata yayi a mota ya figi motan dakarfi. To be continue....

Bai nufi ko inaba sai gidansu da ita. Adda da alh suna falo. Tashigo dafarko adda bata ganetaba anma data shigo sai ta ganeta sosai. Kuka ne murna ne? Bakinta na rawa tace basant?. Kece.? Alhaji ma a tsorace yamike. Itakam kallonsu take batare datasan mesuke nufiba. Tacewa ahmed suwaye wannan?. Yakalleta saida gabansa yafadi adda ne ta rungume ta tana kuka. Basant tace nifa banganekiba. Adda a firgice ta dago tare daja baya. Baki ganeniba?. Ni mahaifiyarki?. Haba basant . Kallonsu take kawai. Adda tafadi a firgice suka jata sai asibiti . Kiri kiri dai sukaga haikam basant bata ganesuba hakan yasa alhaji. Nemo malami aduba. Yana kallonta yace asiri akayi. Kuma mai karfi. Suka kalleshi sukace kaman yaya kenan. Yace donda gashin kan mahaifinta dakuma na mahaifiyarta akahada. A tsorace alhaji yace tayaya? Ahmed yayi murmishi yace ta ruky. Alhj yace banganeba. Anan ahmed ya ware musu komai. Jikinsu yayi sanyi lalle kabar dan adam ayanda yake. Inbadon ahmed baya karyaba da alhaji zai iya karya tashi. Adda tasamu sauki . Anma basant kam wani firgici tafara da gurnani. A falle tabankadesu tafara gudu(aikin asirin. Don boka yace ko tatafi wani gu dole tadawo garesu)
Binta yayi dagudu tana fizga tana wani gurnani. Wanda duk mai imani inyaganta dole ya tausaya mata. Malam yace zamu karya asirin donhaka dole a tsareta haka adda naji tana gani aka daure basant. Sannan gashi malam yace kar abari su ruky susan tana gunsu kar suje sukara wani sabon shiri. Dakyar ahmed ya lallabi adda karta nunawa rukayya a fuska Haka kuwa akayi. Dayamma sai ga ruky tashigo tana kadadi kamar yadda tasaba. Adda duk kokarinta data danne anma saidata canja fuska. Ruky tace adda lafiya?. Tace kala, Ina tunanin basant dinane. Rukyn tace kikara hakuri hajiya zaa sameta insha Allah. Kuma jikina yana bani tana raye cikin kwanciyan hankali. Kallonta kawai adda takeyi tana mamakin irin makirci da fuska biyu irinna ruky. Ahmed ma dayaxo bai nuna mata komai ba. Yana kam shirye shiryen yadda za'a kamosu ne. Dare malam yakira alh. Yace akwai kwai dasuka ajiye a kwalba a boye. Sai anfasa kwalban asiri zai tonu. Alh. Ya dada rikicewa to shi ainama zai samu kwalban. Wayansa yacire yadannawa ahmed kira . Cikin minti kadan saiga ahmed din yazo. Zuwansa keda wuya yagaya masa abinda ake bukata. Ahmed yace abu mai sauki. Dama daren yau zamuje kamosu.
*Dare yayi sunshirya tsaf jamian tsoro aka nufi gidan basamude . Saida suka kewaye gidan tsaf sannan suka shiga anan akaga basamude kam ya damko wata yar mutane. Aka kwada mishi sanda a firgice yadago ganin mutane akansa ya matse tare dacewa lafiya? Kun shigomin gida kaman wanda nayi sata. Ahmed yace mekayi inba satan ba?. Ya kalleshi zaiyi magana ahmed ya kwadeshi anan yasa aka daureshi. Suka bincika gidan sama da kasa dakyar suka samo kwalban da malam yamusu kwatance aka tattaresu akayi office dasu.


To be continue....







Feel Free To Comments Here...

No comments:

Post a Comment