Saturday 21 May 2016

Halaccin Sarauta episode 14 May 21st 2016

Read previous episodes of Halaccin Sarauta episode 


Continuation of Halaccin Sarauta episode 14

zama yayi dirsham babu irin tunanin dabaiyiba aransa, yasan dai kome yasameta. Bazata taba barin garin batare data cimma burinta ba a dan sanin daya mata, macece mai tsayuwa akan raayinta, nan kuma takara bashi tsoro domin kuwa yasan tabbas bazata bar mahaifiyarsa ba,gida yakoma yatara dogarai yabasu cikiyanta, har cikiya da hotonta idan amsamu wanda yaganta zai samu kaso na dukiya mai soka Aliya kuwa tuni tasamu tanemi hayan gida ciki da falo, taje tasiya sabbin furnitures, da kayan kallo da duk wani abu datasan yana wancan gydan tabari, saidata koma gaba daya sannan hankalinta yakoma kan yadda zatasamu damanjuya fada batareda sungantaba, tayi iya tunaninta anan ta tuna da bilki, toh tayaya zatayi magana da bilki babu yusuf?

Dole shikadai zai iya dauko mata ita, inbahaka bilki bazatabar fada ba, ko acikin matan sarkin bawacce tafi kusanta balle tanemi alfarma, tsaki taja tasako dan riganta iya gwiwa da jeans, tadaura dankwalin akanta batayi kama da yaran hausawa ba ko kadan wanda tayi hakanne donta batar da kammani, yanayin garin yamata dadi sosai yadda take tafiya duk wanda zai ganta zai tabbatar da macece marar son damuwa da tashin hankali, masara tagani ta ciro gudan dubu daya a aljihunta tamikawa matan, matan tamika mata guda daya da canji aliya taki karba haka tabar mata canjin, matan tabita da godiya, hankalinta a kwance tanaci tana tafiya can taga taro andan cika dasauri tanufi gun, wasu ne suke fada ana kokarin rabasu ganin mazane ba yadda ta iya tajuya tatafi, har gyda taje sannan ta kwanta akan kujera taji dadin dan zaga garin datayi koba komi tayi exercise din kafa, buga kofa taji anyi batareda tunanin komi ba tamike tabude ga mamakinta saitaga ysuf, mayar da kofan tayi zata rufe atake yasako hannunsa bahali dole tabari, tana juyawa takama kanta tareda cewa"mekazoyi?"

Cikin murna da farinciki ji yakeyi kaman ya rungumota yace "yazaayi bazanzo ba. Naxo gaysheki ne" tana zama tadauko wani takarda tana dubawa tareda cewa "mutanen garinnan munafukai ne, har anje anfadamaka inda nake, fitan danayi ko awa biyar banyiba" bai amsa ta ba illa zama dayayi yana kallonta, ta ajiye littafin tareda cewa "taimakona zakayi, inaso kadaukomin bilkisu akwai maganan dazamuyi" ganin tadage yace "maganan yadda zaki kashe babana da mamana?" Ta mugun tsorata anma tadanne tareda yin murmushi tanacewa "mesukamin? Babu , donhaka ni tambayan bilki kawai zanyi!" Yamike tareda cewa bazaki ganta ba nasan menakeyi, so kike kiyi amfani dani wurin ramakon ki ko?" Ganin datayi tamkar yasan komi ta tabbatar dacewa lallai yakaranta littafinnan donhaka tabata rai tareda cewa "ae!" Baiyi mamaki ba, dama yasandole zaa rina, abunda zatace kenan, yamike tareda cewa "kinemi wani hanyan ramakonki badaniba, sannan kiyi adduan Allah yarufe bakina akanki" yana fada yabar gydan, ko ajikinta don tasan bazai fadaba, dazai fada tun tana baiwarta zaifada, tayi zama tana tunanin hanyan dazatabi duk iya tunaninta dole yusuf ne hanyan, inbai taimaka mataba babu yadda zatayi, gashi yariga dayasani tasan zaibi duk wani hanya domin yaga ya tsayar da ita, wanda aganinta bazai taba faruwa ba, donhaka dole tabi hanya daya, wato ta ajiye komi tajanyo yusuf ajikinta har yasota wanda bazai iya mata musu ba, wani zuciyan tace toh yanzumman yaaka kare?

Donhaka bari tagwada tagani Kwanansa uku bai lekota ba, tana hankalce anma tana adduan Allah yasa yazo din, domin zuwanshi ne kadai mafita agareta, cikin ikon Allah dayamma kamar yadda takeyi, yau kuma dogon rigane ajikinta tadaura dankwalin taje cin masara, harta karbi masaran taji murya abayanta yanacewa shima abashi, juyawan dazayi taganshi, bata kulashi ba takarba tafara tafiya wanda yana binta abaya sanye yake da kannanun kaya sunyi asalim yimasa kyau, kowakallonsu yake domin ba karamin kyau sukayiba,tayi kaman batasan akwai mutum agunba har sukaje kofan gydan tabude tashiga yabiyota, bata kulashiba tacire dankwalin gashin yazubo tazauna tamike kafafunta alamun tagaji, tanaji yana kiran sunanta tashareshi tamkar bada ita yake ba, ganin ta mayar dashi mahaukaci yanufi kanta kwalban coke dake hannta yakarba yawurga akasa tas tafashe, aliya bata dago ta kalleshiba balle ta tambayeshi, ganin zata haukatar dashi yasa yanufi kanta ganin zaimata hauka tasa kafa ta tokareshi hawaye ne a idonsa " don Allah kiyi hakuri duk zuciyan dakikayi dani kiyi hakuri, baxan iya rayuwa ba keba, wlh inasonki aliya kefe madafar zuciyata, na yadda ko meye zakiyi dani kiyi, kiyi amfani dani zanyi biyayya inhar zaki gwadamin so, komi kikeso zanmiki in bilkisu ce barin aika akirata" yamike zai fita tace "yarima!" Yajuyo yakaleta sannan tace " kainake son kaje kadaukota dakanka" ba musu yace "toh

To download Inside Arewa application for easy access follow the link

No comments:

Post a Comment