Wednesday 4 May 2016

Halaccin Sarauta Episode 8 4th May 2016

Continuation of Halaccin Sarauta Episode 8

Aliya ta runtsa sannan tace "mekakeso dani?!" Cikin rashin damuwa yace "kenake so" bata kalleshiba tadauko towel, tashiga toilet tajiko da ruwan sanyi, tana zuwa ta maka masa dasauri yace "awhsh meye haka?" Fuska a murtuke tace "danna kace kana so!" Tana fada tana danna masa kafan lumshe ido yake cikin dadi don shikam har ransa yadda yakejin sanyin haka yakeji aransa, sonta yake don jiya dakyar yayi bacci tun taimaka masa datayi take idda mishi gizo, mintsinansa tayi bashiri yabude ido, "meye haka?" Yadda yabata rai, saikace meshirin kashe barawo, bata kulasa ba tamike tareda cewa "nagama" tajuya zata fita , samata kafa yayi tuni ta tuntsire tayi kasa, cikin tausayi yace "wayyo kiyi hakuri " bata kulashiba tamike tafice, dadi yaji aransa. Itakuwa inbanda kwashe masa albarka ba abunda take a zuciyanta, fannin yakolo tanufa, jiki dasauki hamdallah, shima don sarkin yadauko malamai sukayi saukan qurani, sannan malamin yayita bayani " wannan adduan dakuke rainawa ance kunayi kunaga kaman wasane,kuyi zikirin safe dana yamma ,Allah yana kareku, fatiha,falaq da nas , ayatul kursiy,ga lailaha illa anta subhanaka inni quntum minal zalimin, lailaha illalahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku walahul hamdu wahuwa ala kulli shay in qadr, akwai su dayawa kunemi hisnul muslim shine makamin mumini, duk sharri da asiri da jinn Allah zai kareku, inhar kanayi kuma kaga wani abu yasameka toh kadauka wannan kaddara ce kuma jarabawa, don annabi SAW anyi masa asiri kuma takamashi, anma kuma yakarya. Don haka dole kuyi imani da kaddara, ku yarda Allah shiyake komi, babu yadda zaayi dan wani abu yasameki saiki bude baki kice wacce ce tayimin haka, a a nikam anmin asiri, zato zunubi, Allah bayason haka, duk abinda yasamu mumini anaso kayi imani kakuma fuskanceshi, zama kace anmaka asiri kana biye biye ba daidai bane, safe da yamma ko yaushe ka kasance da adduanka," yakalli jakadiya tare dacewa "abasa qur'an" tamika masa yakalli qur'anin gashinan dai anma sai kura alamun cewa andade ba a budeba, yace "toh kunga wani matsalan meye amfanin fansar quranin da zaa ajiye don ado?,ba gwara kubayar sadaqa a masallatai ba?,sai kuga agyda ansiya qur'an sama da goma, an ajiye wato acemuku musulmai kuba arna bane, ina amfanin haka baka karanta qurani, anma kullum zaa kunna tv, zaa hau whatsapp, facebook, wata inbatahau ba kaman zatayi zazzabi, zaatashi tsakar dare ayita waya kuma sai akwanta goshin asuba, anmanta da Allah waiyazubillah, yakamata duk mu tsarkake ranmu, bature yazo mana dawani cuta mai wuyan magani,duk wannan social media din cutane, Allah ya tsaremu, yakuma kara mana imani, anma dole mucanja inhar munaso muga mai kyau, rashin bin Allah da dokiknsa shike sawa muke ganin jarabawa kala kala, " duk kowa jikinsa yayi sanyi sarki kansa yaji wannan waazin don yamanta wen last yabude qurani, gwara sallah yanayi dukka a masallaci anma baya farilla, falmata kuwa wacce tazo daga baya , bindin shedan tamanta wen last tayi sallah, donkuwa a maganin da akabata an umurceta da kartayi sallah na kwana arbain, donhaka take zuane, yakolo kuwa baiwar Allah wacce tayi imanin jarabawa take fuskanta agun ubangiji taji dadin jawabin malam ko ba komi zai kara mata tuni da mutuwa dakuma kwanciyan kabari, bayan anwatse aliya tanufi dakinsu tasamu bilki wacce ita tana kwance tana hutawa tamike tareda cemata "matan sarakuna yaushe zasu kara zuwa?" Bilki tace "ran laraba menene?"aliya tace " babu kawai inason sanine" dadi taji ganin plans dinta yana tafiya daidai.
Godiya ga Benazir data rubuta mana wannan labarin. Zamu cigaba insha Allah ranar sati mai zuwa.

No comments:

Post a Comment