Monday 20 June 2016

Halaccin Sarauta episode 27 S Monday 25th June

Halaccin Sarauta episode 27

To read the previous episodes follow the link HERE 

Tunaninsa duk yajuya, alokacin suka nufi fannin da aka kwantar da sufyan abdullahi ne ke zaune agefensa inda yake zura masa ido sufyan yayi murmushi sannan yace "karka damu, zageni kawai raina baxai baci ba," hakan yasa abdullahi ya makeshi dakarfi tareda cewa "soko, wawa!ka cuceni wlh, kacemin harda ita a rasuwa meyasa ka boyemin tana raye?"sufyan bai damu da zagin ba yace "yazama dole ne,dole in boye wa duniya wacece ita, ko so kakeyi itama abimin ita akashe?" Shidai abdullahi baice komi ba yasan cewa abun yanaciwa sufyan rai shiyasa baiyi wani rikici ba har suka sallameshi daga bed rest din dasuka bashi alokacin sukaje dubata, tafarka anma ta jigata sosai, har ranta taji haushi asalin haushi taji don tabbas tasan cewa tanada matsalan kidney tanemi nasayarwa ko zata siya asaka mata tafasa daga baya acewanta kar tazo tafara ciwo bata cika burinta ba, gwara tagama idda cika burinta kafin ta kwakulo wani ciwo gashi yanzu sun nemo, kuma sunaso sucire tasan duk yadda zatayi suhakura bazasu hakura ba dole tabari su saka, fatanta Allah yatada kafadunta don ta cimma burinta Sufyan ne da abdullahi suka shigo dakin ta tsaya ne taga ko zataga yusuf bata ganshiba nan da nan zuciyanta ya sosu sosai, abdullahi kuwa saiyake ganinshi kaman bakon mutum agareta, kaman bakon fuska, tayaya zaifara fuskantarta?

Shikam yadawo ruwa tsundum!, zama sukayi agefe sufyan yariko hannunta cikin tausayi, yanason kanwarsa gani yake itace sauran bangaren jikinsa, ganin basuda niyya magana ta bude baki da kyar sannan tace "meye haka kaman na mutu!" Sufyan yayi murmushi tareda cewa "bazaki mutuba ko raina zan iya cirewa nabaki don na sadaukar dakaina agareki"abdullahi hawaye ne ke zuba masa a ido anma yanata kokarin yaga yadanne yashare saboda kar agane, duk lokutan dasuka kasance tare suna yara yatuna, yatuna lokacin daya mata alkawarin zama da ita ko wani hali na rashi ko samu, yamata alkawarin taimakonta cikin kowani hali ko da kuwa zai rasa ransa ne, cikin sanyin murya yace "yajikinki?" "Dasauki ranka shi dade" a karo na farko kenan dayaji wani iri data kirashi haka yasan ada takan ce masa "yayana" bazai iya zama ba bai amsata ba yafice yabar dakin waje yafita yashiga motarsa kuka yafarayi sosai, tunda yataso yayi wayo baiyi kukan dayayiba, nadama duk ta isheshi, toh ni benaxir damuwan meyakeyi?

Aiba laifinsa bane, yusuf ne yashiga dakin alokacin inna tagama jimaminta tana zaune itama agefe shidai sufyan yaki motsawa, yusuf yazauna agefe tareda cewa "yajikin?" Bata amsa shiba anma ta gyada masa kai, hakan yasa yaja gefe yazauna duk yadamu, likitan ne yashigo don dubata bayan dube dube yace sufyan yazo su gwada kidney dinshi, yabi likitan inda sukaje akayi scanning aka duba kidney dinshi da lafiyansu sannan ko shima zai iya badawa wani bayan dogon bincike likitan yakirashi kanshi a sunkuye yana cewa "kayi hakuri sufyan, bazaka iya bawa aliya kidney dinkaba saboda kaima naka basuda isheshen lafiya," wani dogon salati inna tayi sufyan kam daskarewa yayi agun, yagagara motsi shikan hankalinsa yatashi, yazaiyi da rayuwansa? Anan yafara rokon likitan yakawo dabara ataimakawa yar kanwarsa anan likitan yakawo shawarar akira yusuf, nan da nan suka kirashi atake ya amince zaibayar inda akace yashiga don amasa scanning shima, bayan ankammala likitan yace washegari zasuji result tunda dare yayi, hankalinsu duk yatashi innace ta kwana a asibitin abdulahi da yusuf suka koma gyda, ko yusuf dayaga falmata zata dameshi fitowa yayi yabar masu gidan, Washegari karfe tara anty ta iso asibitin yusuf, abdullahi da sufyan suma duk suna gun, likitan yakirasu inda yabawa yusuf hakuri cewa "yusuf you are not a donor donhaka bazaka iya bataba, kidney dinta bazai karbi naka ba" tunda sufyan yake baitaba fuskantar tashin hankali irin wannan ba baisan sanda yafara fidda hawaye da gumi ba, yusuf kam kuka yake wiwi, yarasa yazaiyi anan duk suka fito abdullahi yagagara tafiya, hankalinsa yatashi office din yakoma tareda cewa "dr. Kidney dina guda dayace tayi saura, ko akwai hanyan dazan iyabata ? Tunda kunce agobe kukeso!," Likitan yakalleshi alaman mai tababben hankali sannan yace "kayi hakuri kanaso ka mutu ne?" Cikin tsawa abdullahi yace "meruwanka da mutuwa ko rayuwata! Kagayamin hanyan dazanyi"cikin tsoro likitan yajawo files dinsa sannan yace "Inhar zaka bada sauran kidney dinka zakadawo bakadashi ko daya, toh munada dialysis machine wanda yake aikin da kidney yakeyi, dashi zakana amfani har lokacin da jikinki zatayi resistn ," abdullahi yayi hamdallah sannan yace duba kagani ko zan iyabata inyaso kacire ayau dinnan kanemo danwanka zanbiya ko nawane, kusamu kusamata kozata sami lafiya, sannan karka yadda kafadawa kowa!"

Likitan ya tsorata shikam yakasa gane kansu, gashi dai danuwanta bazai iya bada nashiba, yusuf kuma falmata ce ta aiko wa asibitin wasika cewa karsu yadda su dauka nashi susawa wata banzar bawa ko dukkansu zasu rasa aikinsu, hakan yasa duk suka tsorata suka cemasa nasa bazai karbu ba, ga abdullahi mai mata anma ya yanke shawaran yahakura da duniya, dahaka yaduba yaga komi daidai atake yayi magana da likitan dazasu cire, adaren ranan suka cire masa kidney dinshi kwaya daya, masha Allah sadaukarwar soyayyaya da cika alkawari tabbas abdullahi yanuna nagarta da hallacin sarauta, yanuna cewa inhar baicika alkawari a matsayinsa na masoyinta ba albarkar sarautar gydansu zaisa yacika, yagwada mata cewa agydansu yatashi da nagarta, baimanta da alkawarin tun suna yara ba yau yacika. Yacika mata alkawarinsa nacewa zai tsaya agefenta, zai taimaketa koda kuwa zaizama ajalin rayuwarsa, acikinmu mutane nawane suke cika alkawari? Sufyan kuwa yana wata duniya daban don neman kidney dazaasa wa aliya shida yusuf sai kiransu akayi aka sanar dasu abdullahi yabayar yusuf dayake tuki saidayayi wawan reverse yatsaya sanin cewa abdullahi kidney dinshi dayace tarage suna nufin yabada wannan? Lalle kam akwai rikici, abdullahi nason aliya? Innalilahi yazayi?

To be continue....

Godiya ga Benazir data rubuta wannan labarin.

No comments:

Post a Comment