Tuesday 29 May 2018

An Sanya Wa Katafaren Asibitin Da Sanata Shehu Sani Ya Gina Sunan Balarabe Musa

An Sanya Wa Katafaren Asibitin Da Sanata Shehu Sani Ya Gina Sunan Balarabe Musa

Da yake jawabi a yayin bikin bude Asibitin wanda ya gudana a Unguwar Bagado Kamazoo yankin Karamar Hukumar Chikum ta Jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewar la'akari da halin kunci da kuma takura da Jama'ar yankin ke ciki dangane da batun kiwon lafiyar su, ya sanya shi zabura wajen gina musu Asibiti na zamani domin amfanin su da 'ya'yansu harma da jikoki wadanda za su zo anan gaba.

Sanatan mai wakiltar shiyyar Kaduna ta tsakiyan ya kuma kara da cewar, ya sanya wa Asibitin sunan Dattijo tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, bisa ga irin kokarin da Dattijon ya ke da shi na kishi gami da taimakon talakawa inda ya bayyana shi a matsayin abin koyi ga Shugabanni na kwarai.

Da yake tofa albarkacin bakin shi dangane da muhimmin aikin da Sanatan yayi, Dattijo Balarabe Musa ya bayyana jin dadi gami da farin cikin shi akan kwazo da kokarin Sanata Shehu Sani, wanda ya bayyana shi a matsayin wakili nagari kuma Shugaba wanda ya damu da damuwar Jama'ar shi, sannan ya kara da cewar irin su Shehu Sani sune Shugabanni nagari wadanda suka dace da suja ragamar Al 'umma, wadanda ba su damu da tara abin duniya ba, babban abinda ke gaban su shine yadda za su tsamar da Jama'ar su daga halin damuwar da suke ciki.

Mista Adamu Giwa shine Sarkin Kauyen Bagado, ya mika godiyar Jama'ar shi ga Sanatan wanda suka bayyana shi a matsayin Mutum Karimi wanda baida nuna wariya ko wani bambanci a tsakanin jama'a, domin a tarihin garin nasu na Bagado babu wani Dan siyasa da ya taba kai musu dauki sai a wannan karon da Sanata Shehu Sani ya share musu hawaye, a bisa ga wannan dalilin su basu da wani Shugaban da za su zaba a yankin Kamazoo da Karamar hukumar Chikum, karamar hukuma mafi girma a jihar Kaduna mallakar Kabilar Gwari, sai Sanata Shehu Sani.

Sanatan Kaduna ta tsakiyan ya kuma jagoranci kara bude wasu manyan Asibitoci guda biyu wadanda ya gina a garin Gadagau dake yankin Karamar Hukumar Giwa, da kuma daya Asibitin dake garin Gadani ta Karamar Hukumar Igabi.
Dukkanin Al'ummomin yankin Kananan Hukumomin Uku da aka zanta da su, wato Kananan Hukumomin Giwa da Igabi da kuma Karamar hukumar Chikum, Kananan Hukumomi uku daga cikin Bakwai wanda Sanatan ke wakilta a Majalisar Dattawa, sun bayyana cewar ba su da wani Dan takara da za su zaba sai Sanata Shehu Sani a kakar zabe da ke tafe ta 2019.

Al'ummar Jihar Bauchi Sun Yi Gangamin Nuna Goyon Bayan Tazarcen Gwamna M.A A Zaben 2019

Al'ummar Jihar Bauchi Sun Yi Gangamin Nuna Goyon Bayan Tazarcen Gwamna M.A A Zaben 2019

Dandazon al'umma a jihar Bauchi wadanda suka hada maza da mata a jiya Litinin sun yi gangami zuwa fadar gwamnatin jihar domin nuna goyon bayan su ga gwamna Barista M.A Abubakar, inda suka jaddada cewa ba su da wani dan takara da ya wuce gwamnan M.A a zaben 2019.

A yayin jin ta bakin jagoran gangamin, Kabir G. Kobi Dan Hajiya, ya bayyana cewa sun yi gangamin ne domin kara jaddada goyon bayan su ga Maigirma Gwamnan Jihar Bauchi, Barista Mohammed Abdullahi Abubakar.

Da yawa daga cikin masu zanga-zangar sun bayyana cewa kasancewar sun gamsu da salon mulkin Barista M.A, babu abin da zai sanya su juya masa baya a zaben 2019.

Dalilin Da Ya Sa Zan Sake Tsayawa Takara A Zaben 2019— Ganduje

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya tabbatar da cewa zai sake tsayawa takara a zaben 2019 don kammala ayyukan da ya fara.

Ya ce, tuni wasu mutanen kirki a jihar suka nuna masa sha'awarsu na ya sake tsayawa takara inda suka tanadar masa Naira milyan biyar don sayen fom na yin takarar.

Monday 28 May 2018

SAMA DA NERA MILYAN DARI DA RARARA YAYI SAMA DA FADI DASU ASHE FILIN KWALLO YAJE YANA GINAWA A KAUYEN KAHUTU

Daga JARIDAR DIMOKURADIYYA:

Bayan fara gudanar da bincike ana zargin kudaden da Dauda Kahutu Rarara yayi sama da fadi dasu sama da nera milyan Dari na kungiyar mawaka kauyen su Kahutu yaje yana gina filin kwallo na zamani.

Kafin lokacin Kungiyar Gwamnonin Jam'iyyar APC ta basu nera milyan 15 su bude ofishi wanda kudaden suka fada akawunt din Dauda Rarara, sai dai kawai ya kira mu yace mana ya kama ofis a (Gwamna Road) dake jihar Kaduna kuma kudaden ma duka sun kare, haka ya kama ofis din babu sanin shugaban kungiyar da matemakin sa da kuma membobin kungiya; inji Yala

Bayan an bude ofishin kungiyar, kungiyar Gwamnonin Jam'iyyar APC ta hannun Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari su suka bayar da kudade a matsayin tallafi, kuma Aminin Dauda Rarara Isyaku Oris ya tabbatar mun an baiwa Rarara nera milyan 100 yanzu haka suna akawunt din sa;inji Ibrahim Yala matemakin shugaban kungiyar

Da Dauda Rarara da Baban Chinedu da Isyaku Oris su suka fara tafiya maganar kudaden amma da za'a koma bai koma dasu ba.

Ibrahim Yala yace yanzu haka idan muka kira Rarara a waya baya dauka a kan maganar kudaden a saboda haka nayi shawarar saka Yanjaridu a cikin maganar 'Tunda farko nina kwana da sanin cewar Dauda ba tsakanin da Allah yake so a bude wannan kungiyar ba, yana so ne yayi amfani damu kawai'.

Saboda kin yarda daya yi azo a zauna kan kudin shi yasa aka fara zargin da kudaden yaje yana gina (Stadium) a kauyen su Kahutu dake jihar Katsina.

Har yanzu da bazata Buhari yake rawa-Tsohon Shugaban Kasa Jonathan

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan ta bakin Mai ba shi shawara kan kafofin sadarwa na zamani a wancan lokaci Reno Omokri yace sai da Jonathan ya kirkiri fiye da ayyuka 1000 kuma ya kammala su sarai a lokacin mulkin sa wanda daga ciki akwai tsarin BVN.

A jawabin na tsohon Shugaban kasar ya hada da yi wa Adams Oshiomole raddi bayan ya zargi Gwamnatin sa da satar dukiyar Kasa.

Jonathan yace shi ya gyara filin jirgin sama na Garin Enugu ya kuma kirkiro sababbin Jami’o’i har 12.

Bayan nan Jonathan yace daga cikin ayyukan sa akwai gina Makarantun zamani na Almajirai da kuma kawo tsarin You Win da GIS domin Matasa.

Har wa yau Jonathan yace shi ya kawo wasu hanyoyin dogo da kuma tituna a Kasar.

Duk da kiran tsohon Shugaban barawo, Omokri yace gidajen da tsohon Gwamnan Edo Adams Oshiomole ya gina sun fi na Jonathan kyau, duk da cewa Jonathan din ya rike Najeriya kuma kafin nan ya rike kujerar Gwamnan Jihar Bayelsa.

Buhari Yayi Watsi Da Tsarin 'Almajiri School' Tanko Yakasai

Tsohon dan siyasa kuma uba a wannan kasa Tanko yakasai ya bayyana cewa yankin arewancin kasar nan na fuskantar kalubale tare da matsaloli ne sakamakon halin ko in kula da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke yi game da tsarin karatun Almajirai wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya aiwatar.

Ko me Yasa Buhari Be Damu da Halinda Almajirai Suke Ciki ba?

NI ISIYAKU ORIS DA DAUDA RARARA MU MUKA JE MUKA KARBO NERA MILYAN 100 A HANNUN ABDULAZIZ YARI



Daga JARIDAR DIMOKURADIYYA:

Matemakin shugaban kungiyar mawaka Ibrahim Yala yace Isiyaku Oris ya tabbatar mishi da cewar Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari nera Milyan 100 ya baiwa Dauda Rarara ba nera milyan 60 ba.

Isiyaku Oris wanda tare suka je Wajen Gwamnan Jihar Zamfara kuma shima yana daya daga cikin mawakan kungiyar yace tabbas an baiwa Rarara kudin kungiya kuma suna hannun shi nera milyan 100.

Ibrahim Yala Wanda shine matemakin shugaban kungiyar mawaka yace yanzu idan suka kira Dauda Rarara a waya baya dauka saboda maganar kudade "kuma tun lokacin da Rarara ya bukaci mu hada wannan kungiyar na gane cewar so yake yayi amfani damu; Motocin kungiyar mu duka suna hannun shi yana ta amfani dasu.

Tunda farko shugaban kungiyar Haruna Aliyu Ningi yace Rarara yace mishi nera milyan 60 kawai aka bashi kuma daga ciki milyan sittin din ya baiwa wadanda suka yi hanya kudaden suka fito nera milyan 18, kuma ragowar nera milyan 42 da suka rage suna akawut dina kuma akawut din ya sami matsala.

To amma yanzu an tuntubi Dauda Rarara yace shi bai ma san da maganar wasu kudade ba.

Dauda Rarara a wata hira da yayi da wani Danjarida yace shi babu wanda ya bashi ne goma.

Rashin Tsaro: Abin Kunya Ne Yadda Ake Buga Misali Da Nijeriya — Jonathan


Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana  cewa abin kunya yadda a halin yanzu kasashen duniya ke buga misali da Nijeriya a matsayin kasar da Harkokin tsaro suka tabarbare.

Jonathan ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da bude wata gada da Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya gina inda ya bayar da misali da Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo wanda a kwanan nan ya yi izgilanci ga hukumomin Nijeriya kan rashin tabbatar da tsaro.

Gwamnan M.A Yana Iyaka Kokarinsa Wajen Aiyukan Ci Gaban Jihar Bauchi, Cewar Mataimakinsa Da Ya Yi Murabus

.... Gwamnan Bauchi ya amince da karin albashin ma'aikatan kiwon lafiya a jihar

"Kamar yadda na baiyana a cikin takardar bari na aiki, na ajiye aikina ne don bisa ra'ayina. Ina kira ga al'ummar jihar Bauchi da su rungumi gwamnatin jihar Bauchi domin cigaban jiha.

"Ban ajiye aiki na don wata manufa ba, kawai na ajiye aikina ne kasancewar na kudiri aniyar wa'adi daya zanyi akan kujerar mukaddashin gwamnan jihar Bauchi.

"Ban ajiye mukamina don tozarta gwamnati ba kamar yadda wasu ke fassara hakan, na ajiye mukamina ne kawai don kaina kuma har gobe ina tare da gwamnatin jihar Bauchi. Ina kira ga dukkan maison cigaban jihar Bauchi da ya marawa gwamnati baya domin cigaba da aiyukan alkairi wa jihar Bauchi", mamar yadda Injiniya Gidado ya bayyana.

A gefe daya kuma, Gwamnatin Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Mohammed A. Abubakar, ta amince da biyan ma'aikatan kiwon lafiya albashin su na tsarin nan na ma'aikatan kiwon lafiya, a jihar Bauchi.

Gwamna M.A  ya amince da biyan wannan kudi kaso dari cikin dari da ma'aikatan suka jima suna neman a aiwatar musu da shi na tsarin nan na (CONMESS) da kuma na tsarin (CONHESS) na ma'aikatan kiwon lafiya na jihar bauchi

Wannan sanarwan karin data fara aiki ne a wannan wata na mayu na shekaran 2018

Mai tallafawa Gwamnan jihar Bauchi akan harkokin sadarwa Alhaji Shamsuddeen Lukman Abubakar shine ya shaidawa manema labarai hakan.

'Yan Ta'adda Sun Kashe Mutane 27 A Jihar Zamfara

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a Zamfara inda suka kashe mutum 27 a karamar hukumar Maradun.

'Yan bindigar sun kai harin ne a ranar Juma'ar da ta gabata cikin yankin Gidan Goga da ke karamar hukumar Maradun.

Tsohon kwamishinan watsa labarai na jihar Alhaji Ibrahim Dan malikin Gidan Goga ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar wasu matasa ne a yankin da suka dauki bindigogi suka shiga daji.

"Sun iske manoma suna shuka da safe suka bude masu wuta bayan sun yi gargadin a kauracewa yin shuka a gonakin yankin," in ji shi.

Ya ce lamarin ya kara muni bayan da 'yan banga suka yi kokarin kai dauki, inda 'yan bindigar suka kara kashe wasu mutane baya ga manoman da suka kashe da farko.

Me ya sa babu wanda ya damu da rikicin Zamfara?Zanga-zangar matasa kan yawan kisan mutane a Zamfara

Tsohon kwamishinan ya ce yawancin mutanen kauyukan da ke yankin, bugaje ne makiyaya da ke rikici inda suke zargin juna da sace-sacen shanu, kuma yanzu rikicin ya shafi hausawa manoma.

Ya ce an tura jami'an tsaro bayan da al'amarin ya faru kuma sun janye daga yankin bayan an yi jana'izar wadanda suka mutu.

Jihar Zamfara dai na cikin jahohin arewa maso yammaci da ke fama da yawaitar kashe-kashe da sace-sacen mutane da dabbobi.

Gwamman mutane ne suka mutu a 'yan watannin da suka gabata sakamakon hare-haren da aka kai wasu kauyuka a jihar ta Zamfara.

Daruruwan mutane aka kashe a Zamfara a tsawon shekaru shida da aka kwashe ana fama da matsalar tsaro a jihar.

Sanata Kwankwaso Ya Raba Jari Ga Matasa Sama Da Dubu Uku


Daga Khadija Garba Sanusi

Sanatan Kano Ta Tsakiya, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya raba jari ga matasa 3007 dake mazabarsa.

An yi bikin raba jarin ne a yau Lahadi a dakin taro na 'THE AFFICENT' dake kan titin Magajin Rumfa a cikin garin Kano.

Koda a watanni biyu da suka gabata Sanatan ya rabawa mata zalla na mazabar tasa su 5000 jari kyauta.

Sunday 27 May 2018

Gidaje Fiye Da 100 Sun Ruguje Sakamakon Guguwa Mai Karfi A Karamar Hukumar Gumel Dake Jihar Jigawa

Gidaje Fiye Da 100 Sun Ruguje Sakamakon Guguwa Mai Karfi A Karamar Hukumar Gumel Dake Jihar Jigawa

Sakamakon Guguwa Mai Karfin Gaske Yayi Sanadiyar Rugujewar Gidaje Fiye Da Dari A Cikin Unguwar Dan Tanoma Dake  Garin Gumel  Jihar Jigawa.

Tuni Shugaban Karamar Hukumar Gumel Hon. Aminu Sani Gumel  Ya Tura Wakilci Daga Majalissar Zartawa Karamar Hukumar Gumel Domin Duba Irin Barnar Da Guguwar Tayi, Tare Da Jajantawa Al'umma Da Iftila'i Ya Samesu.

Shugaban Karamar Hukumar Yayi Matukar Jimami,Da Nuna Damuwarsa,Ganin Yadda Iskar Ta Shafi  Sama Da Gidaje Dari.

A Karshe Cikin Alhini, Karamar Hukumar Gumel Ta Jajantawa Al'ummar Da Abin Ya Shafa,Tare Da Kira a Gare Su Cewa Su Dauki  Wannan A Matsayin Wata Jarraba Daga Ubangiji.

Sannan Karamar Hukumar Gumel Karkashin Jagorancin Za6a66en Ciyaman Hon Aminu Sani  Tayi  Alkawarta,Cewa Insha Allahu Zatayi Bakin Kokarinta  Domin Mika Al'amarin Ga Hukumar Agajin Gaggawa Ta Jaha,Domin Kawo Musu Tallafin Gaggawa.

RAMADAN: Sheik Zakzaky Ya Raba Kayan Abinci Ga Mabukata

Daga Ammar Muhammad Rajab

Kamar yadda ya saba a duk shekara a lokacin azumin watan Ramadana, tun kafin gwamnati ta kama shi, Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, yana raba kayan hatsi wadanda suka hada da Masara, Gero, Shinkafa, Suga da sauran su a irin wannan lokacin. Shekara na uku kenan (duk da yana tsare) a jere duk da Shehin Malamin gwamnatin Nijeriya na ci gaba da tsare shi, amma Shehin Malamin ya ci gaba da wannan aikin alherin ga al’umma.

A bana ma kamar kowacce shekara, an raba hatsin a inda aka saba rabawa a cikin Unguwanni na cikin karamar Hukumar Sabon gari da Zariya wanda ya hada da: Unguwannin Sabon gari, Unguwan Gwado, Hayin Ojo, Dogarawa, Tohu, Samaru, Shika, Likoro, Chikaji , Muchiya, Tudun Wada, Tudun Jukun, Zariya cikin gari, Dan Magaji, Unguwan Dankali, Wanka da sauransu.

Rabon na bana, an fara shi tun daga farkon watan Ramadanan nan har ya zuwa yau 11 ga watan Ramadan ba a kammala ba. Hakazalika a bana rabon ba a garin Zariya kadai ya isa ba, an raba a garin Kaduna. A bangaren Abuja kuwa, an raba a Mararrabar, Karmajiji, Gwarinfa, Suleja, Masaka, Gwagwalada, Lugbe da sauransu.

Idan mai karatu bai manta ba, shekaru kusan Uku ke nan, gwamnatin Nijeriya na rike da Shehin Malamin, duk da kuwa wata babbar kotun Nijeriya a karkashin mai shari’a Gabriel Kolawale ta ce a sake shi a kuma biya shi diyyar naira miliyan 50 shi da matarsa bisa tsare shi da aka yi ba da hakki ba, kuma a gina masa gida a duk inda yake so a Arewacin Nijeriya, amma har yanzu gwamnatin ba ta bi wannan umurnin ba.

Wa Zai Zama Sabon Halifan Tijjaniyya A Nijeriya?

Daga Yusuf Ibrahim Yakasai (BBC Hausa)

Tun bayan rasuwar Halifan Tijjaniya a Najeriya da kasashe makota Shaikh Isyaku Rabi'u, hankula suka fara karkata kan wanda zai gaji matsayinsa a darikar, wacce ke da dimbin mabiya.

Kawo yanzu dai mabiya darikar ta Tijjaniyya na ambata wasu shugabanni da ake ganin sun cancanci matsayin.

Sai da alama za a iya samun sabanin ra'ayi tsakanin 'yan Tijjaniyya, kasancewa kusan kowa na da nasa gwanin.

Ko da a lokacin da aka bawa Shaikh Isyaku Rabiu matsayin ma, wasu shugabannin darikar kamar Shaikh Dahiru Bauchi sun nuna rashin amincewa.

Kuma bayanai sun ce tuni ma wasu suka fara bayyana sha'awar matsayin.

Asalin halifancin Tijjaniyya a Najeriya

Halifancin darikar Tijjaniyya ya fara ne bayan shekarar 1963 lokacin da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na daya ya bar sarautar Kano ya koma Azare da zama.

A lokacin ne jagoran darikar ta Tijjaniyya na duniya Shaikh Ibrahim Nyass ya nada Sarki Sanusi a matsayin halifansa a Nijeriya.

Shaikh Inyas ne ya fara nada Sarki Sanusi na daya (na farko daga dama) a matsayin halifansa a shekararun 1963 bayan ya bar sarautar Kano

Shaikh Dahiru Bauchi ya shaida min cewa a shekarar ya hadu da Shaikh Nyass a birnin Makka a lokacin aikin Hajji, kuma ya ba shi sako wajen Shehunan Tijjaniyya a Najeriya musamman ma Kano da kuma Sarki Sanusi (wanda a lokacin ya koma Azare bayan barin sarautar Kano), cewa ya nada shi halifansa.

"Duk mai son ziyarata, to ya ziyarci Sanusi" In ji Shaikh Nyass, kamar yadda Shaikh Dahiru Bauchi ya fada.

Daga baya ne bayan ya dawo daga aikin Hajji, Shaikh Nyass ya aiko da takardar nada Sarki Sanusi a matysayin halifansa.

Nada Shaikh Isyaku Rabiu Khalifa

Khalifa Isyaku Rabi'u ya fuskanci kalubale bayan nada shi a matsayin Khalifan Tijjaniya a 1995.

Tun bayan rasuwar Khalifa Muhammad Sanusi a 1990, ba a nada wani a matsayin ba sai 1995 lokacin da jikokin Shehu Tijjani daga Maroko suka nada Isyaku Rabi'u a matsayin halifa.

Sai dai matakin ya haifar da takaddama tsakanin manyan darikar, inda wasu shugabanni kamar Shaikh Dahiru Bauchi suka nuna rashin amincewa da nadin.

Shikh Dahiru Bauchi ya shaida min cewa Shaikh Nyass ne kadai ke da ikon nada halifa, kuma tunda a lokacin ba ya raye, babu wanda ke da ikon nada wani a matsayin halifan Tijjaniyya.

Don haka, wasu ma na ganin Shaikh Isyaku Rabi'u sai dai ya zama halifan Sarki Sanusi, amma ba halifan Tijjaniyya ba.

To sai dai tun bayan nada Isyaku Rabiu, malamin ya rungumi al'amuran darikar ka'in da na'in, musamman wajen kashe kudi, da yi wa jikokin Shehu Tijjani da 'ya'yan Shehu Nyass hidima.

Abubuwa hudu da za a iya tuna Khalifa Isyaka Rabi'u da suYadda rayuwar marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u ta kasance'Ba a bukatar wani halifa yanzu'

Rasuwar Shaikh Isyaku Rabi'u ta sake bude wata kofar ta neman halifancin darikar, abin da ke nuna cewa duk wanda aka nada tamkar shi ne jagoran mabiya darikar a Najeriya.

Wasu jagororin darikar na ganin babu bukatar nada wani halifa, tunda batun halifancin ba ya cikin sharuda ko ka'idoji na darikar ta Tijjaniyya.

Babban limamin masallacin Abuja Shikh Ibrahim Ahmad Maqri na ganin batun halifanci a darikar ta Tijjaniyya ba wani abu ne mai muhimmanci ba, abin da ya ke mafi muhimmaci shi ne kiyaye ka'idojin darikar da yin aiki da su, da kuma hada kan jama'a.

Shaikh Maqri ya ce ko da nadin da aka yi wa Sarkin Kano Sanusi I "dalili ne na addini, dalili ne zumunci, dalili ne na karfafar 'yan uwantaka, da kuma rage damuwa na abin da ya faru da Khalifa Sanusi".

To amma ganin yadda zamani yake sauyawa da kuma yadda aka shafe shekaru sama da 20 'yan darikar ta Tijjaniyya suna daukar Shaikh Isyaku Rabi'u a matsayin jagora zai yi wuya yanzu su zauna ba tare da jagora ba.

Wa zai karbi mukamin a yanzu?

Tuni dai wasu a darikar suka fara yunkurin neman wanda zai zama sabon Khalifa, kuma da alama za a iya kai ruwa-rana.

Shaikh Dahiru Bauchi.

Shaikh Dahiru Bauchi ya ce ya wuce a ce za a nada shi halifancin Tijjaniyya a yanzu, domin tuni Shehu Inyass ya nada suYana daga cikin almajiran Shaikh Ibrahim Inyass 'yan kadan da suka rage a rayeTun a zamanin Shikh Inyass yana cikin mutanen da ke kare darikar Tijjaniyya da yadataShaikh Inyass da kansa ya ambace shi "Kakakin Faida (Lisanul Faidati)"Mahaddacin Al-kur'ani ne kuma yana daga cikin manyan malamai a NajeriyaWasu na ganin shekarunsa sun ja don haka bai kamata a kara masa wani nauyi ba

To amma a tattaunawar da muka yi da shi Shaikh Dahiru Bauchi ya ce shi ba ma ya bukatar matsayin, domin kuwa tuni Saikh Inyass ya nada shi halifansa tare da wasu manyan darikar.

"Ai ni na wuce nan, Shaikh Ibrahim da kansa ne ya nada mu halifofi mu, kuma shi kadai yake da iko ya dauki daya daga cikinmu ya daura a kan mu gaba daya," in ji malamin.

Ya kara da cewa, "Shi halifa a cikin Tijjaniyya kamar janar ne a cikin soja, ba guda daya ba ne, don haka kowa ya san wanda ya fi shi."

Wasu jagorori a darikar Tijjaniyya na ganin Shaikh Dahiru Bauchi ba ya ma bukatar wani nadi na musamman, duba da irin matsayinsa a darikar da yadda yake da mabiya, da kuma iliminsa.

Sarkin Kano Muhammad Sanusi II

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na daga wandada ake ganin sun cancanci matsayin halifancin tijjaniya a Najeriya, matsayin da asali kakansa ne ya fara rikewa.

Asalin mukamin dai na Sarkin Kano Sanusi na daya ne, wato kakan sarki na yanzu. Sarkin Kano na yanzu ya kama harkar darikar sosai bayan ya zama sarki. Ya taba bayyana cewa gwaninsa shi ne Sarkin Sanusi na daya, kuma yana so ya gaje shi. Yanzu yana da mulki da kudin da zai iya yi wa darikar hidima fiye da wasu shugabannin da damaYana da ilimin addini da na zamani, kuma yana kara samun karbuwa a tsakanin wasu musulmin NajeriyaYa ci gaba da jagorantar zikirin Juma'a da ake yi duk shekara a gidan Sarkin Kano, wanda aka fara a zamanin Marigayi Ado Bayero.

Wasu bayanai na nuna cewa tuni wasu mabiya darikar da kuma wasu makusantan sarkin suka fara nuna cancantarsa.

Shaikh Shariff Ibrahim Saleh

Wani babban jagoran da ake ganin ya kamata ya zama jagoran mabiya darikar ta Tijjaniyya a Najeriya shi ne Shaikh Shariff Ibrahim Saleh Alhusayniy.

Yana daga cikin manyan malam darikar Tijjaniyya da Musulunci baki dayaYa yi karatu a wajen manyan malamai sama da 300 a kusan dukkan kasashen musulmai na duniyaYa yi karatu a wajen Shaikh Inyass, kuma wasu na yi masa kallon daya daga manyan almajiransaWasu na ganin ya fi kowa cancantar zama jagoran darikar a Nijeriya

To amma malamin bai fiya shiga cikin al'amuran shugabanci ba, ya fi maida hankali wajen karantarwa da rubuce-rubuce da bada fatawa da kuma tafiye-tafiye.

Don haka wasu na ganin ko da an yi masa tayi da wuya ya karba.

Da gaske ne Shehu Ibrahim Nyass ya bayyana a Maulidin Abuja?Ganin Shehu Ibrahim Nyass karama ce - Dahiru BauchiAikin da ke gaban sabon jagoran Tijjaniyya a Najeriya

Nijeriya ita ce kasar da ta fi yawan jama'a a nahiyar Afirka, kuma yawan mabiya darikar a kasar ya zarta na kowacce kasa a nahiyar.

Kuma saboda muhimmancin da Shehu Inyass ya nuna na kasar a fuskar darika, ya sa wasu ke kallonta a matsayin cibiyar darikar bayan Maroko da Senagal.

Don haka duk wanda zai zama jagora tamakar ya dauki nauyin 'yan darikar ne a kasar da wasu kasashe makwabta kamar Nijar da Ghana da sauransu.

Shaikh Maqari na ganin babban abinda ya kamata ya sa a gaba kamar hada kan 'yan darikar da sauran musulmin kasar, musamman wadanda suke da sabanin fahimta.

Yace kuma dole ne sabon jagoran darikar ya maida hankali wajen nisanta darikar da bara-guri da suke aikata wasu abubuwa da suka ci karo da addinin musulunci, kuma suka fakewa da sunan darikar.

Wasu malaman darikar kuma na ganin dole ne a yi cikakken nazari kafin a zabo wanda zai zama jagoran darikar.

Malamai kamar Shaikh Nura Muhammad Arzai na cewa dole a samu mai jajircewa, tsayayye, mai kamewa mai tsayawa a kan manufa.

Ya ce ana bukatar mai cikakken ilimi na addini da na zamani.

Malamin ya kara da cewa ana bukatar sabon jagoran ya zama yana da wadata da zai iya kamewa daga abin hannun mutane, kuma zai iya daukar nauyin gudanar da al'amuran darikar.

A yanzu dai za a zuba ido a ga yadda za ta kaya musamman ganin irin tasiri da mukamin ke da shi a darikar ta Tijjaniya.

Darikar Tijjaniya a takaice

An kafa darikar ne a kasar Aljeriya a shekarar 1784. Sheikh Ahmad ibn Muhammad al-Tijjani ne ya kafa ta. Ta yadu zuwa sassan duniya daban-daban, inda ta ke da mafi yawan mabiyanta a Arewaci da kuma Yammacin AfirkaTana kuma da karin mabiya a Afirka Ta Kudu, da Indunisiya da kuma sauran sassan duniya. Akwai sauran dariku na Sufaye a addininin Musulunci amma Tijjaniya ta fi kowacce girmaSun ce suna da muhimman ayyukan ibada guda uku a kowace rana:Neman gafarar Allah; Yin salati ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma kadaita AllahSai dai ana zarginsu da wuce gona da iri wurin nuna soyayya ga Shehunnansu, lamarin da wasun su ke musanta waAna alakanta Sheikh Ibrahim Nyass da farfado da darikar a karni na 20 bayan ta kwanta damaAn haife shi a kasar Senegal kuma jama'a kan yi tattaki daga sassan nahiyar da dama domin ziyartar kabarinsaDarikar Tijjaniya ta kasu kashi-kashi musamman a kasashe irin su Nijeriya inda suke da mabiya sosai.

Shehu Sani da Hunkuyi suna gab da ficewa daga jam'iyyar APC, dalilansu...

Wani bangare na jam'iyyar APC da ke karkashin jagorancin Sanata Suleiman Hunkuyi da ke wakiltar Kaduna ta arewa da Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya sun ce akwai yiwuwar za su fice daga jam'iyyar.

A wata sanarwa da suka fitar a jiya Juma'a, sanatocin biyu da ke kiran kansu da suna APC Akida sunce sun kammala bita akan jam'iyyar da matsalolin shugabancin da ke adabar jam'iyyar a jiha da ma kasa kuma suna tunanin ficewa daga jam'iyyar da suka taimaka wajan kafawa.

APC Akida ta ce za ta dauki matakin ficewa ne "Idan babu wata kwakwarar alamar samun nasara wajen magance matsalolin wariyar da kuntatawa da ake yiwa wasu yan jam'iyyar a jihar Kaduna"

Shugaban kungiyar, Tom Maiyashi, wanda ya fitar da sanarwar ya ce akwai wasu abubuwa guda biyu da suka faru a jihar wanda suka tabbatar masa da cewa babu shugabanci na gari a jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna kamar yadda The Cable ta rawaito.

"Yadda aka gudanar da zabukan shugabanin jam'iyya da kuma zabukan kananan hukumomi a jihar ya tabbatar min da cewa rashin jagoranci mai kyau zai dushe duk wani farin jini da jam'iyyar ke dashi a jihar."

Dama dai kungiyar APC Akida ta bayyana yiwuwar faruwar hakan tun da fari lokacin da ta lura da irin kamun ludayin gwamna Nasir El-Rufai," a cewar Maiyashi.

A saboda wannan dalilan ne kungiyar ke kira ga duk wadanda gwamna El-Rufai ke ganin girmansu da su hanzarta jan kunnensa domin kare jam'iyyar daga fadawa cikin bala'i.

Kungiyar kuma ta sanar da mahukuntan jam'iyyar a jiha da kasa cewa za su fice daga jam'iyyar idan har ba'a yi gyara ba.

Matasa biyu sun mutu wajan murnar sakin Jonah Jang

Bayan da kotu ta bayar da belin tsohon gwamna  jihar Flato, Jonah Jang,
magoya bayansa da dama ne suka tare shi suna nuna murnarsu da wannan saki da aka mishi,

matasa daga yankin Tudun Wada na jihar sun rika wasa da mota akan tituna dan nuna murna inda aka samu tsautsayi har biyu daga ciki suka mutu.

Sirfwang Kefas da Jerry Sunday na daga cikin wadanda ke nuna irin wannan murna yayin da suke cikin mota ana tukin ganganci dasu, motar ta kwacewa direban inda ta kauce hanya dalilin haka matasan biyu suka rasa rayukansu, kamar yanda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Matasa da dama ne suka fito suna nuna goyon baya ga Sanatan wanda ake tuhumarshi bisa barnatar da kudi sama da biliyan shida.

Rarara Ya Awon Gaba Da Kudin Kungiyar Mawaka Har Naira Milyan Dari


JARIDAR DIMOKURADIYYA

Anyi cirko-cirko a Ofishin kungiyar mawaka tun bayan bullar rahoton mawaki Dauda Kahutu Rarara yayi kwana da makuden kudade sama da nera milyan Dari.

Shugaban kungiyar mawakan na yankin Arewa Haruna Aliyu Ningi dake jihar Bauchi shiya bayyanawa manema labaru, yace Gwamnan Jihar Zamfara shiya basu kudin bayan sun bukacin hakan kan irin gudun mawar da suka bayar a gabanin zabukan 2015 gashi kuma sun shirya bayar da gagarumar gudun mawa a zabukan 2019 dake tafe.

Tunda farko Dauda Rarara shiya shige gaba wajen karbo kudaden kuma ya tabbatar mun da cewar Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya fara basu nera Milyan Sittin sai dai wadanda suka yi hanya har aka bayar da kudaden ya basu nera milyan goma sha takwas inji Haruna Ningi.

Ya kara da cewar a matsayina na shugaban kungiya har zuwa yau Dauda bai taba yi mun maganar ba, bayan lokacin dana sake tun tuba sa sai yace har yanzu ba'a cika ragowar kudaden ba amma na kusa dashi wanda shima yana daga cikin mawakan mai suna Oris yace tuni an baiwa Rarara ragowar nera milyan Arba'in din.

To a hakan dai muka bukaci nera milyan Arba'in da biyu da suka rage a hannun shi ya kawo su azo a zauna a tattauna a kan su sai yace wai asusun ajiyar shi na banki ya sami matsala.

Buhari Ya Soke Kwangilar Makaman Isra’ila Ta Dala Miliyan 195

Shugaba Muhammadu Buhari ya soke kwangilar nan ta sake sayo kayan tsaro, wadda ministocin sa suka kirkiro, saboda zargin harkalla a cikin kwangilar.

Kwangilar wadda Ministocin suka sa wa hannun a cikin watan Disamba, 2017, an rattaba cewa za a bai wa kamfanin kwangilar mai suna HSLi zungurutun kudi har dala milyan 195, shi kuma zai kawo jiragen yaki da helikwafta da kuma jirage kanana na yaki na ruwa, 12 daga Isra’ila.

An ce Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ne ya shirya kwangilar, yayin da masu sukar lamarin suka ce an kirkiri kwangilar ne domin a saci kudade kawai.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari ne ya rubuta wa Antoni Janar na Najeriya, Abubakar Malami wasika cewa a soke kwangilar.

Sannan kuma Buhari ya umarci mai ba shi shawara kan harkokin tsaro da kuma hukumar liken asiri ta kasa da su binciki yadda kamfanin ya samu yarjewar yin kwangilar ba tare da samun satifiket na gangariyar amincewa da tabbacin ko sahihancin yay i kwangila a kasar Isra’ila ba.

Sannan kuma Buhari ya bada umarnin cewa kamfanin kwangilar ya kawo kayayyaki na dala miliyan 50, wato na adadin kudin da aka fara ba shi a matsayin somin-tabi tun kafin ya fara kawo komai.

Binciken da Arewa Dailypost ta gudanar ya nuna cewa kamfanin HSLi ba shi ma da rajista a kasar Isra’ila, amma sai ya hada baki da wani kamfani na kasar Isra’la mai suna Mitrelli, wanda aka ce kamfanin ya na da alaka ta kusanci da Minista Ameachi.

Cikin 2012 a lokacin da Ameachi ke gwamnan jihar Rivers, ya taba bai wa Mitrelli kwangilar aikin wata gona a can gefen Fatakwal har ta tsabar kudi dala milyan 140.

A da can babu ruwan Mitrelli da harkar makamai, amma a dare daya kamfanin ya tsoma kan sa a cikin kwangilar makamai.

An gurfanar da dan Atiku a gaban kotu saboda ya gaza biyan alawus din 'ya'yan sa

A ranar Larabar data gabata ne wata babbar kotu da ke zamanta a Igbosere jihar Legas ta saurari karar da aka shigar a kan, Aminu Atiku, dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar saboda rashin biyan kudin kulawa da yaransa N250,000 duk wata da bai biya ba tun watan Fabrairun 2018.

Sai dai Aminu Atiku ya shaidawa Alkali kazeem Alogba cewa yana daukan dawainiyar duk bukatu na yaransa.

Mai shari'a Alogba zai zartas da hukunci a kan wata bukata da Atiku ya shigar a kotun inda ya ke rokon a janye kudin wata na kulawa da yaran da kotu ta gindaya masa a baya.

Kotun ta tsayar da cewa a rannan ne zata zartas da hukuncin bayan jin muhawarrar da lauyan Atiku, Oyinkan Badejo da kuma Ethel Okoh, lauyan tsohuwar matarsa,Ms Ummi Fatima Bolori suka tafka.

Atiku da tsohuwar matarsa Bolori duk basu samu halartar kotun ba.

A karar da ya shigar,Aminu Atiku yana rokon kotun ta canja hukuncin da wata kotun ta zartar a baya inda aka dankawa tsohuwar matar rainon yaransu Ameera mai shekaru 11 da kuma Aamir mai shekaru 7.

Da aka fara sauraron karar a ranar Larabar, Badejo ta bayyana cewa akwai alamar tambaya a kan biyan N250,000 a kowanne wata da aka dorawa Aminu Atikun duk da cewa yana daukan nauyin dawainiyar yaran.

A cewarta,Aminu Atikun yana dauke dukkan nauyin yaransa wanda suka hada da biyan kudin makarantarsu tare da kudin magani da sauransu.

Lauyan ta ce kotun da ta yanke wannan hukuncin ba ta yi la'akari da karfin aljihun Atikun ba shi yasa ta dora masa N250,000 a duk wata, ta kara da cewa bai dace ayi la'akari da dukiyar da iyayen Aminu Atikun suka mallaka ba.

Sai Lauyan Bolori, Okoh ta kallubalanci wannan zancen.
Ta ce tun da Atikun bai biya kudin kulawa da yaran ba tun watan Maris, inda ta kara da cewa rashin biyan kudin kulawa da yaran ya sabawa sashi na 62(5) na dokar kiyaye hakkin yara.

Ta yi ikirarin cewa Atiku bai biya kudin makarantar yaransa ba sai ranar 11 ga watan Afrilu, kwana daya kafin kotun ta saurari karar.

An gurfanar da dan Atiku a gaban kotu saboda ya gaza biyan alawus din 'ya'yan sa

A ranar Larabar data gabata ne wata babbar kotu da ke zamanta a Igbosere jihar Legas ta saurari karar da aka shigar a kan, Aminu Atiku, dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar saboda rashin biyan kudin kulawa da yaransa N250,000 duk wata da bai biya ba tun watan Fabrairun 2018.

Sai dai Aminu Atiku ya shaidawa Alkali kazeem Alogba cewa yana daukan dawainiyar duk bukatu na yaransa.

Mai shari'a Alogba zai zartas da hukunci a kan wata bukata da Atiku ya shigar a kotun inda ya ke rokon a janye kudin wata na kulawa da yaran da kotu ta gindaya masa a baya.

Kotun ta tsayar da cewa a rannan ne zata zartas da hukuncin bayan jin muhawarrar da lauyan Atiku, Oyinkan Badejo da kuma Ethel Okoh, lauyan tsohuwar matarsa,Ms Ummi Fatima Bolori suka tafka.

Atiku da tsohuwar matarsa Bolori duk basu samu halartar kotun ba.

A karar da ya shigar,Aminu Atiku yana rokon kotun ta canja hukuncin da wata kotun ta zartar a baya inda aka dankawa tsohuwar matar rainon yaransu Ameera mai shekaru 11 da kuma Aamir mai shekaru 7.

Da aka fara sauraron karar a ranar Larabar, Badejo ta bayyana cewa akwai alamar tambaya a kan biyan N250,000 a kowanne wata da aka dorawa Aminu Atikun duk da cewa yana daukan nauyin dawainiyar yaran.

A cewarta,Aminu Atikun yana dauke dukkan nauyin yaransa wanda suka hada da biyan kudin makarantarsu tare da kudin magani da sauransu.

Lauyan ta ce kotun da ta yanke wannan hukuncin ba ta yi la'akari da karfin aljihun Atikun ba shi yasa ta dora masa N250,000 a duk wata, ta kara da cewa bai dace ayi la'akari da dukiyar da iyayen Aminu Atikun suka mallaka ba.

Sai Lauyan Bolori, Okoh ta kallubalanci wannan zancen.
Ta ce tun da Atikun bai biya kudin kulawa da yaran ba tun watan Maris, inda ta kara da cewa rashin biyan kudin kulawa da yaran ya sabawa sashi na 62(5) na dokar kiyaye hakkin yara.

Ta yi ikirarin cewa Atiku bai biya kudin makarantar yaransa ba sai ranar 11 ga watan Afrilu, kwana daya kafin kotun ta saurari karar.

PDP ce ta tsiyatar da Najeriya,- Oshomole

Tsohon gwamnan jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomole ya sake yiwa gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shagube inda ya ce idan da za'a rabawa dukkan 'yan Najeriya kudaden da ake zargin gwamnatin Jonathan ta karkakatar ,da kowa ya zama attajiri a kasar.

Tun a baya, Oshiomole ya dade yana cacakar gwamnatin Jonathan a kan zargin karkatar da kudaden Najeriya.

Oshiomole ya yi wannan furuci ne a jiya Juma'a yayin da ya ke jawabi ga shugabanin jam'iyyar APC na jihar Edo.

Yace ,Aljihun kowane 'dan Najeriya zai cika ya batse idan da za'a raba musu kudaden da aka karkatar zamanin Jonathan

Osjomole ya ce ,dole ne a rika jaddada irin mulkin da gwamnatin PDP ta kwashe shekaru 16 tana yi wanda hakanne ya jefa Najeriya cikin talauci da fatara.

Ya ce jam'iyyar APC a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari tana kokorin ceto yan Najeriya daga cikin halin kuncin da PDP ta jefa kasar.

"Hakkin hakkinmu ne mu magoya bayan jam'iyya mu fadakar da mutanen karkara wadanda suka jefa mu irin halin da muka shiga a yau da kuma kokarin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari keyi don ceto mu, wanda hakan yasa yan Najeriya a yanzu sun fara alfahari da kasar," inji Oshiomole.

Tsohon gwamnan ya cigaba da cewa ya kamata mutane su fahimci irin wahalar da ke tattare da yin gyara a gidan daya ruguje saboda daura turbar sabon gini da kammala ginin ba abu ne da za'a iya kammalawa a dare daya ba.

A cikin yan kwanakin nan ne Oshiomole ya nuna sha'awarsa na tsayawa takarar kujerar shugabancin jam'iyyar APC inda kuma ya kara da cewa shugaba Buhari ne zai lashe zabe saboda irin nasarorin da ya samu a yanzu.

Thursday 24 May 2018

A lokacin da nake mulkin Soji bana jin shakkar kowa – Shugaba Buhari

A jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da ‘Yan kungiyar BSO ta Magoya bayan sa a fadar Shugaban kasar da ke Aso Villa inda ya tattauna da su kan batutuwan da su ka shafi halin kasar.

Buhari yace IBB ya saki barayin da ya daure kuma aka zauna lafiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamnatin sa na matukar kokari duk da halin da ta tsinci kan Kasar nan.

Shugaban Kasa Buhari yake cewa babu Shugaban kasar da ya kashe kudi wajen gina titi da hanyoyi irin sa.

Shugaba Buhari yace Gwamnatin nan ta kashe sama da Tiriliyan 1.3 cikin bara da bana kurum domin gina hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa a Najeriya.
Inda Kafin nan dai an bar tituna da hanyoyin dogo sun lalace kwarai a Kasar.

Bayan haka Shugaban kasar yace a lokacin da yake mulkin Soji sai da ya kama duk Shugabannin kasar ya daure saboda zargin sata illa wanda ya iya karbar kan sa.

Sai dai yace a wannan tsarin Damukaradiyya sam hakan ba zai yiwu ba.

Shugaba Buhari yace da yake mulkin Soja tsakanin 1983 zuwa1985 har Shugaban kasa sai da ya daure.
Sai dai kuma bayan an kifar da Gwamnatin sa, sai da aka daure shi kansa sannan kuma aka maidawa barayin kasar duk kudaden da suka sata.

DAN DAZON AL'UMMAR JAHAR KANO KENAN SUKE GABATAR DA SALLAR AL'KUNUT A KOTU YAYIN DA AKA GURFANAR DA SARDAUNAN KANO

DAN DAZON AL'UMMAR JAHAR KANO KENAN SUKE GABATAR DA SALLAR AL'KUNUT A KOTU  YAYIN DA AKA GURFANAR DA SARDAUNAN KANO

A Yau Alhamis aka kawo Malam Ibrahim Shekarau {SARDAUNAN KANO}  A babbar KOTUN Gwamnatin tarayya dake KANO

Dan dazon jama'ar kano ne suka fito domin nuna bakin cikin su da hakan

Kasancewar An jibge jami'an tsoro domin hana mutane shiga kallon shari'ar hakan yaba jama'a damar yin SALLAR AL'KUNUT akan TITI,  sallar an gudanar da ita maza da mata harda wadanda ba yan jam'iyyar SARDAUNAN KANO ban

Zuwa yanzu a na gabatar da Shafi'u, sai dai  abun jira a gani shine ko za'a bada su beli

Daga yanzu laifi ne aurar da macen da bata haura shekaru 18 ba - Gwamnatin jihar Borno

Gwamnatin jihar Borno ta sanar da cewa duk wanda aka samu ya aurar da diya mace da bata balaga ba wato bata shekara 18 ba laifi ne kuma duk wanda gwamnati ta kama da aikata hakan zai fuskanci fushin hukuma.

Gwamnan jihar, Kashim Shettima ne ya yi wannan gargadi a ranar Laraba yayin ya ke jawabi ga iyayen yara da ke amfana da shirin samar da ilimi kyauta ga yara da gwamnatin jihar ta kaddamar.

Gwamnatin jihar kuma ta bawa iyayen yaran kyaututuka wanda suka hada da kayayakin abinci, tufafi don kara musu gwarin gwiwa na tura yaransu mata zuwa makaranta a maimakon aurar da su tun kafin su girma.

Shettima ya ce: "Ku kyalesu su kammala karatun sakandare, ko mun baku taimako ko bamu baku ba, duk wanda aka kama ya aurar da diyarsa mai shekaru 12 zai fuskanci hukunci.

"A matsayinmu na iyaye, ya zama dole mu taimakesu su samu ilimin boko da addinin musulunci," inji gwamnan.

Mafi akasarin fulanin da ke zaune a garin yan gudun hijira ne wanda suka baro gidajensu a yankin tafkin Chadi. Kafin gwamnati ta kaddamar da samar da ilimin kyauta, mafi yawancin fulanin basu tura yaransu makarantar boko.

Sai dai a yanzu, gwamnatin ta wayar da kansu game da fa'idojin da ke tattare da ilimin boko musamman ga yaransu mata.

A kalla yaran fulani 600 neke amfana daga shirin bayar da ilimi kyautar.

A cewar gwamnatin jihar, za'a samar wa fulanin da suka rasa muhallinsu gidajen da za su zauna.

Ana sa ran za'a ware gidaje 100 daga cikin wanda attajirin dan kasuwa Aliko Dangote ya gina a matsayin gudunmawarsa ga wadanda rikicin ta'addanci ya ritsa da su.

An bukaci Shugaba Buhari ya cunawa Obasanjo da Jonathan hukumar EFCC

Wata kungiya mai zaman kanta a Najeriya dake rajin kare martabar dan adam da kuma tabbatuwar demokradiyya watau Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) a turance ta bukaci gwamnatin tarayya da ta soma binciken tsaffin shugabannin kasar Najeriya game da yadda suka tafiyar da harkar wutar lantarkin kasar.

SERAP a cikin wata sanarwa da ta fitar ta rabawa manema labarai, ta bayyana cewa abun takaici ne a kashe kusan dalar Amurka biliyan 16 a harkar wutar lantarkin amma har yanzu ba ta canza zane ba.

Daga nan sai kungiyar ta shawarci shugaban kasar da ya mika tsaffin shugabannin kasar ga hukumomin binciken da suka kamata domin gudanar da bincike a kan su.

Mataimakin Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus

Mataimakin Gwamnan jihar Bauchi, Nuhu Gidado ya yi murabus inda ya nuna cewa bai sha'awar aikin.

Ragwaye Ne Masu Kukan Yunwa A Gwamnatin Buhari, Cewar Shugaban Kwastan Hameed Ali

Ragwaye Ne Masu Kukan Yunwa A Gwamnatin Buhari, Cewar Shugaban Kwastan Hameed Ali

Shugaban hukumar Kwastam ta Nijeriya Hameed Ali ya ce mafi akasarin ‘yan Nijeriya da ke kukan yunwa a karkashin gwamnatin shugaba Buhari ragwaye ne da basu da karfin zuciyar tashi domin neman na kansu.

Shugaban na Kwastam ya bayyana haka ne, yayin da ake karin haske dangane da nasarorin shirin gwamnatin Najeriya akan bunkasa ayyukan noma a kasar, a wata ganawada yayi da kungiyar magoya bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke Abuja.

A cewar Hameed Ali, babu yadda za ayi abinci ya rika fadowa mutane daga sama, dan haka ya zama tilas mutane su tashi tsaye domin amfani da damarsu wajen neman abin rufawa kai asiri.

Dangane da shugabancin Buhari kuwa, shugaban na kwastam ya ce kaunar Najeriya da ‘yan kasar ne ya sanya shi fafutukar karbar jagorancin kasar duk da cewa shekarunsa sun haura 70.

Ali ya kara da cewa inda shi ne ya ke da yawan shekarun shugaba Buhari, ga fansho mai kyau da gidansa na zama a Daura, ba zai dorawa kansa nauyin da zai hanashi sararawa ba ta hanyar shiga siyasa, amma kaunar kasarsa ta sa shugaba mai ci yanke shawarar.

Gwamna Ganduje Ya Jagoranci Musuluntar Da Maguzawa 61 A Kano

Daga Anas Saminu Ja'en

A yau Laraba gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci musuluntar da maguzawa da dama Maza kimanin 21 Mata kimanin su 40, karkashin Gidauniyar Ganduje a babban masallacin fadar gwamnatin jihar.

EFCC Ta Sake Kama Shekarau


▪ Gobe Za A Gurfanar Da Shi Gaban Kotu

Rahotanni daga Kano sun tabbatar da cewa a halin yanzu Tsohon Gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau yana tsare a ofishin hukumar EFCC da ke jihar Kano.

Daruruwan magoya bayan Shekarau ne dai suka yi cincirindo a titin Dandalin mahajjata inda suka yi kokarin hana tsohon gwamnan shiga ofishin EFCC wanda ya isa wurin da misalin Karfe hudu na Yamma, lamarin da ya janyo aka karo jami'an tsaro wadanda suka yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa magoya bayan Shekarau.

A gobe Alhamis ne dai, hukuma za ta gurfanar da tsohon Gwamnan a gaban kotun tarayya da ke Kano shi da Aminu Wali da Mansur Ahmed bisa laifin karbar Naira Milyan 950 daga hannun Tsohuwar Ministar Mai, Alison Deizani Madueke a lokacin zaben 2015. Sai dai Kakakin Tsohon Gwamnan, Sule Sule ya nuna cewa an tuhumi Shekarau ne saboda ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari.

Za A Rusa Gidajen Karuwai Da Na Barasa A Jihar Borno

Gwamnan Jihar Borno Alh Kashim Shettima, ya bada wa'adin kwanaki 10 da a rusa gidan karuwai da wajen holewanan na Galadima dake garin Maiduguri.

Galadima mattara ce ta karuwai, mashaya da sauran lalatattu masu aikata badala da bata tarbiyar al'umma.

Su ma manyan Malaman musulunci na jihar sun sha jan hankalin gwamnati dangane da wannan wuri.

Wannan umurnin ya zo ne kwanki kadan bayan da Gwamna Shettima ya bada dokar korar 'yan cacar NAIJABET a fadin jiharsa.

Daga Comr Mohammed Pulka

Tuesday 22 May 2018

EFCC Ta Kama Tsohon Dan Takara Gwamnan Jihar Sokoto Da Tsohon  Ministan Ruwa Da Wasu 3

EFCC Ta Kama Tsohon Dan Takara Gwamnan Jihar Sokoto Da Tsohon  Ministan Ruwa Da Wasu 3

DAGA CMRD A'B ZUBAIRU 

Hukumar EFCC ta kai wa wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP samame a jihar Sokoto bisa zargin su da karba 500,000000 a shekarar 2015.

Friday 18 May 2018

Shugaba Buhari ya saki kudi domin yashe kogin Kwara don arewa ta karbi jiragen ruwa.

Zaman majalisar kasa na wannan mako, ya sahale sakin biliyoyin nairori, wadanda za'a yi amfani dasu don jawo teku zuwa arewacin kasar nan har zuwa jigar Neja, dama sayo wasu jiragen ruwa da kudin Turai Yuro 21m don jawo jiragen maqare da kaya zuwa arewa.

Ministan Sufuri shine ya bada wadannan bayanai a jiya laraba, bayan zaman na majalisar kasar,
inda ya fayyace yadda za'a fara aikin, wanda a baya shugaba Umaru Musa Yar aduwa ya saki kudi don ayi, amma daga rasuwar sa, wanda ya gaje shi, ya dakile aikin.

Anyi hakan ne don saukaka cunkoso a gabar tekun ta kudu, da saukaka wa arewa shigo da kaya har yankin cikin sauki, inda za'a fara sauke kaya a Baro ta jihar Neja.

Za dai a fadada wasu yankuna na ruwan na Neja, wanda aka baiwa wani kamfani Biara Concept Nig. Ltd.

A gefe guda kuma, za'a samar da gada a garin Karu, sai aikin ruwa a jihar Bauci da Calabar, da wasu manyan tituna da zasu hado kudu da arewar kasar nan.

Yawanci ayyukan shekaru biyu zasu dauka ana yi duk da dai Saura shekara daya wannan zango na mulki ya kare, shuwagabannin su mika mulki ga wasu zababbu, ko kuma su zarce a karo na biyu in an zabo su.

Kwankwaso ba zai iya hana shugaba Buhari cin kano ba – Inji El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi ba'a da shagube ga wasu kusoshin jam'iyyar APC dake barazanar barin jam'iyyar, inda yace barin jam'iyyar tasu bazai hana Shugaban kasa Muhammadu Buhari lashe zabe ba a 2019.

A kwanakin baya dai wasu manyan 'yan siyasa wadanda suka sauya sheka daga PDP zuwa APC a 2014, suka yi zargin cewa an mayar dasu saniyar ware tare da barazanar daukar mataki idan har ba a biya musu bukatunsu ba.

Sai dai Gwamna E-Rufa'i ya yi masu hannunka mai sanda inda yace barinsu jam’iyyar ba zai hana shugaban kasar kawo jihohinsu a 2019 ba.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Talata, El-Rufai, ya ce"tun shekarar 2003 shugaban ke lashe zabe a Kano."Ya cigaba da cewa idan aka yi duba ga yawan mutanen da suka fito saboda tarban Buhari, za a ga cewa Kano wuri ne da shugaban ya ke da magoya baya sosai
Ya kuma ce, wannan gangamin taro ya faru ne ba tare da jama'ar Kwankwaso ba.

Kotu ta dage shari’ar Sanata Dino Melaye har sai baba ta gani

Wata babbar kotun birnin tarayya a ranar Alhamis ta daga sauraron shari’ar Sanata Dino Melaye na jihar Kogi, dagawar da babu wani lokacin sake zama tabbatacce sakamakon matsalar rashin lafiyarsa.

Hukumar ‘Yan Sanda tana karar Sanata Melaye ne a birnin tarayya da kuma garin Lokoja, inda a birnin tarayya suke zarginsa da yunkurin kashe kansa da kuma bata kayan gwamnati, wanda sanadiyar haka aka kwantar da shi a asibiti.

A garin Lokoja kuma ‘Yan Sandan na tuhumarsa da laifin yiwa hukumar karya da kuma bawa ‘yan ta’adda makamai.

Alkalin na birnin tarayya Olasunbo Goodluck, ya bukaci Lauyan wanda ake kara, Rickey Tarfa, ya bayar da kwakkwaran bayani game da rashin bayyanar Melaye a gaban kotun a ranar Laraba, inda ya gabatar da takardunsa na asibiti a gaban kotun.

Sakamakon haka kotun ta gamsu da cewa Mr. Melaye, yana kwance a asibiti bangaren wadanda ake bawa kulawa ta musamman, wanda dalilin hakan ne Alkalin kotun Goodluck ya daga shari’ar dagawa ta har sai baba ta gani.

Najeriya zata hadu da fushin Allah idan gwamnati bata saki El-Zakzaky ba – Sheikh Dahiru Bauchi

Babban malamin nan a Najeriya Sheikh dahiru usman Bauchi yayi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da a zauna domin tattaunawa game da Shugaban kungiyar shi’a El-zakzaky.

A cewarsa ya kamata a samu mafita domin a sake shi ya je ya nemi lafiya, idan har gwamnati tayi haka to lallai babu shakka za'a kara samun zaman lafiya a kasar.

Shehin malamin yaci gaba da cewa kin sakin El-zakzaky wata jarabawa ce da Allah zai jarabci wannan kasar da ita, saboda shugaban shi’an malamine na addinin musulunci, sannan kuma  tsare shi ba tare da wata hujja ba ,kuma ba'a nuna alamar yana da laifi ba ,to lallai Allah zaiyi fushi da wannan kasar.

Sheik Dahiru Bauchi ya kammala bayanansa da cewar malamai dai sune magada annabawa idan aka muzguna masu to babu shakka za'a fuskanci fushin Allah, kuma shi fushin Allah babu dan ba ruwa na kowa da kowa zata shafa.

Daga karshe shehin ya bawa gwamnati shawara data saki El-zakzaky a nema masa lafiya a kasar waje.

Ayyuka miliyan 9 aka rasa a karkashin mulkin Buhari ~Kingsley Mohgalu


Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Farfesa Kingsley Moghalu, yace kayar dashugaba Buhari a zaben 2019 abu ne mai sauki.

Moghalu wanda ke neman takarar shugaban kasa a shekarar 2019 ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, lokacin da yake kaddamar da kungiyar magoya bayansa a garin Awka dake jihar Anambra.

Moghalu yace Buhari ya zubar da mutuncinsa a idon mutanen Najeriya wadanda suka tsaya masa yaci zabe a shekarar 2015.

Yace zai yi amfani da rashin kokarin da Buhari yayi a mulkinsa a matsayin makamin da zai yi amfani dashi don ya kada Buhari zabe a shekarar 2019.

Yana mai karawa da cewa tinanin da mutane keyi na cewa shugaban kasa a shekarar 2019,ya kasance dan arewa wannan rashin tunani ne kuma an kori wannan tunanin ma daga Najeriya.

Sojoji Sun Tarwatsa Mafakar 'Yan Boko Haram A Jihar Borno


Lamarin wanda ya auku a kauyen Abaganaram a jiya Alhamis, bayan kashe 'yan Boko Baram guda biyu tare da kama 11 a raye da sojojin suka yi, sun kuma kwace makamai da dama a wurinsu.

Wani Dan Majalisa Ya Gabatar Da Kudirin Hana Matasa Yin Cacar 'Naija Bet'

DAGA MUKHTAR HALIRU TAMBUWAL SOKOTO

Dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar Sokoto ta arewa ta daya a majalisar Hon Malami Bajare a ranar Laraba ya kai kokensa kan yadda matasa kashi 70 cikin 100 suka tsunduma a cikin cacar naija bet, wadda hakan ya sabawa koyarwa irin ta addinin islama, haka zaliki tarbiyar matasa da dama ta fara gurbacewa a ta dalilin haka.

Ya kara da cewa naija bet caca ce da ta samo asali shekaru dari da doriya wadda aka kirkira domin a hallakar da dubban musulmi, shi ya sa aka sako harkokin wasanni a cikinta domin an san musulmai da yawa suna sha'awar harkokin wasanni musamman kwallon kafa.

Daga karshe ya yi kira da a yi kokarin ganin cewa an dakile wannan wuta da ta taso mai kokarin kona dukkanin tarbiyar da aka san jihar Sokoto da ita, ta hanyar yakar shugabanni wannan lalura.

Muna rokon Allah ya taimaki Malami Bajare akan irin wadannan kudurorri masu amfani da yake kaiwa gaban majalisa.

Wednesday 16 May 2018

NAYI NADAMAR AURE NA FARKO~ Fati Muhammad


Daga Nijeriyarmu a yau

Tsohuwar fitacciyar jarumar nan ta masana’antar Kannywood, Fati Muhammad, ta bayyana auren jarumi Sani Musa Mai Iska a matsayin babbar nadamar ta a rayuwa.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata hira da tayi da Manema labaru inda ta bayyana cewa ta amince da cewa kowa na da jarrabawar da Allah ya ke yi masa sannan kuma tace ita dai jarabawarta ta fannin aure take.

Jarumar ta kara nanata maganarta da tayi a baya inda tace ba fa zata kara auren dan fim ba koma waye.

Daga karshe kuma jarumar ta bayyana jarumi Ali Nuhu a matsayin wanda take darajtawa fiye da kowa a masana’antar fim; kamar yadda majiyar Al'ummata ta wallafa


Idan za ku iya tunawa Fati Muhammad ita ce ta fito a cikin tsohon fim din nan na Sangaya tare da jarumi Ali Nuhu, a matsayin Zubain,
Babu shakka annan fim din ne ya fito da ita.

Ana zargin wani Uba da yayiwa ‘yar cikinsa mai shekaru 15 ciki a Gombe

‘Yan sanda sun gurfanar da Mutuma mai suna Samaila Zakari mai shekaru 50 gaban kotun majistire a jihar Gombe bisa zargin dirkawa ‘yarsa cikin shege.

Rahotan da ‘yan sanda suka gabatar a kotun ya nuna cewa, Mutumin da ake zargi mazaunin garin Deba ya aikata laifin ne ranar 2 da kuma 8 ga watan Mayun da ya gabata, da misalin ƙarfe 10pm na dare yayi lalata da ita ba tare da sanin ta ba.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya shaidawa kotun cewa yanzu haka ‘yar Sama’ilan na ɗauke da juna biyun da yayi mata na watanni biyu.

Wanda ake zargin da aikata laifin yayi amfani da wayo wajen yi wa yarinyar fyaɗe wanda hakan laifi ne da ya saɓawa sashi na 390 da kuma 282 na kundin shari’a. A cewar 'Dan sandan.

Amma sai dai ana shi ɓarin, wanda ake zargi Samaila Zakari ya musanta aikata laifin.

Bisa wannan dalili ne Ɗan sanda mai gabatar da kara ya bukaci da a ɗage shari’ar domin basu damar zurfafa bincike.

Nan take mai shari’a Mr Dorabo Sikam ya karɓi buƙatar hakan, kana ya ɗage shari’ar zuwa 21 ga watan Mayu domin cigaba da sauraron ƙarar sannan ya sanya a tisa keyar wanda ake zargin zuwa gidan Maza.

Anga watan Ramadan a Zamafara da wasu jihohi

Rahotanni daga jahar Zamfara da kuma wasu sassan Nigeria suna bayyana cewa anga jaririn watan Ramadan.

Hausa Times ta ruwaito tuni masallatai a Jihar Kaduna da wasu sassan kasarnan suka fara sanarwa a lasifika domin jama'a su dauki harama. Kazalika Hausa Times ta ruwaito tuni wasu masallatan suka fara gudanar da sallar tarawihi a yau.

Kawo yanzu dai ana dakon sanarwa a hukumance daga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi wanda shi keda hurumin bayar da sanarwa.

Shugaba Buhari Ya Amince A Kashe Naira Bilyan Goma Domin Gyara Yankunan Da 'Yan Ta'adda Suka Lalata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kashe naira bilyan goma don gyara yankunan da hare-haren 'yan ta'adda ya lalata.

Yayin da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo zai sanya ido akan aikin domin ganin an farfado da dukkanin yankunan da aka lalata.

Masu karatu ko me za ku ce akan wannan batu na kashe wannan kudaden?

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri.

Rikici Ya Barke Tsakanin Matasan Binanchi Da Na Iraki A Jihar Sokoto


Daga Mukhtar Haliru Sokoto

Fada ya sake barkewa tsakanin Binanchi da Iraki, inda yanzu haka ana dauki ba dadi tsakanin matasan unguwannin.

Cikin daren jiya ne matasan Iraki fiye da mutane dari dauke da makamai suka lababo inda suka raunata fiye da mutane goma, wayuwar garin yau su kuma suka shirya zuwa daukar fansa.

Dukkanin dauki ba da'din da ake yi a garkar mai alfarma sarkin musulmi ne ake yinsa, Allah ya kawo mana dauki.

MADOGARA MUDASSIRU BINANCHI

Malaman Darika Sun Dace Da Mabiya, Sai Dai Mabiyan Ne Ba Su Dace Da Malamai Ba, Inji Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum

An bayyana cewar a fili yake Shehunnan Darika sun dace da mabiya masu tsananin biyayya a gare su ido rufe, amma su mabiyan ne ba su mori Malamai wadanda za su dora su akan tafarki mikakke na Sunnar Annabi Muhammadu SAW ba, wanda hakan ne dalilin jefa mabiyansu cikin dimuwa da fagamniya a rayuwarsu.

Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah Wa Ikamatus Sunnah na kasa baki daya Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachikum ya bayyana hakan, a yayin da yake tsokaci dangane da ikirarin da 'Yan Darika suka yi na cewar wai sun ga Shehun su Ibrahim Nyass karara a jikin fitilar haska Titi a yayin gudanar da mauludin da sukayi na Shehun a Abuja, a wata tattaunawar da yayi da manema labarai a gidan shi dake Rigachikum Kaduna.

Sheikh Sambo Rigachikum ya cigaba da cewar, ko shakka babu tsananin makauniyar biyayya da kauna ido rufe da 'Yan Darika ke yiwa Shehunnan su ya sanya suka amince da wannan magana, amma maimakon Malaman nasu su fito fili su gaya musu gaskiya, sai suka kara burma su, suka tabbatar musu da cewar lallai Shehu Nyass aka gani cikin fitila, sannan kuma ana ganin shi a wurare daban daban kamar a jikin bango ko a bayan daki ko kuma a jikin madubi da sauran wasu wurare, wanda su kansu Malaman da ke fadin haka sun san ba gaskiya suke fada ba, amma saboda wasu dalilai na son zuciya sai su kayi amfani da jahilcin mabiyan su suka kara kifar da su, " Ai idan akwai wanda ya dace ace ana gani bayan rasuwarshi to Annabi Muhammadu ne, amma babu inda akaji labarin cewar Sahabbai ko Tabi'ai sun ganshi bayan rasuwar shi, a bisa ga wannan da akwai damuwa kwarai da gaske da yadda Malaman Darika ke cutar da mabiyan su ta hanyar cewa ana ganin wani Mahaluki bayan mutuwar shi, idan da ace Malaman Darika za su mayar da hankali wajen karantar da mabiyan su addini yadda yake to wallahi da an samu kyakkyawan cigaba, duba da irin biyayyar da sukeyi wa Malaman nasu, akan haka nake kara jaddada cewar Shehunnan Darika sun dace da mabiya, Mabiyan ne basu dace da Malamai ba " Inji shi.

Dangane da batun Watan Ramadan da za'a shiga ciki kuwa, babban Malamin yayi kira ga Jama'ar Musulmi da su kara gyara halayen su gami da tuba zuwa ga Ubangiji, sannan su kyautata mu'amulolin su da juna, 'Yan kasuwa suji tsoron Allah kada su tsawwala farashin kayayyaki,  sannan Malamai masu Tafsirai su gudanar da Tafsiran su akan tsari da karantarwar sunnar Annabi, a kauce wa dukkanin wani yarfe da huce haushi akan wani, domin Munbarin tafsiri ba fage na banbadanci da tumasanci ba, waje ne na ilimantar da Al'umma Addinin Musulunci.

Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachikum ya kuma yi Addu'a ga Jihar Kaduna da kasa Nijeriya gaba daya na Allah ya zaunar da kasar lafiya, dukkanin fitintinu dake addabar kasar Allah ya kawo saukin su, Allah ya sa mu dace da alkhairan dake cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan, sannan yayi Addu'ar Allah ya Jikan Malamai magabata wadanda suka rigamu gidan gaskiya, kamar su Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Ismail Zakariyya Jos da Sheikh Jafar Mahmud Adam da sauran Al'ummar Musulmi gaba daya.

Mutane Ba Su Da Amana A Yau — Buhari

▪Ba Buhari Kadai Ba Ne Mai Gaskiya — Dogara

Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana cewa a yau mutane ba su dauki cin amana a matsayin laifi ba a maimaikon haka rashin amana ya zama wata dabi'a a tsakanin al'ummar.

Buhari ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da bude sabon hedkwatar hukumar EFCC inda ya ce yaki da rashawa na da matukar wahala saboda ya shafi rassa daban daban na rayuwar al'umma.

A nasa bangaren, Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya yi ikirarin cewa har yanzu akwai milyoyin 'yan Nijeriya wadanda ke da gaskiya da rikon amana ba ya ga Shugaba Muhammad Buhari.

Gwamnati Ta Bada Kwangilar Dala Bilyan 6.68 Na Hanyar Jirgin Kasa Na Kaduna Zuwa Ibadan

Gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin kasar China mai suna "China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC)" na kashe Dala Bilyan 6.68 wajen aikin hanyar jirgin kasa na Kaduna zuwa Ibadan.

Daraktan Yada Labarai na Ma'aikatar Sufuri, Misis Yetunde Sonaike ce ta sanar da hakan inda ta nuna cewa Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi ne ya rattaba hannu a madadin gwamnatin tarayya.

Ganduje Ya Sulhunta Rikicin Majalisar Dokokin Kano


Gwamnan Kano, Injiniya Abdullahi Ganduje ya samu nasarar sulhunta 'yan majalisar dokokin jihar wadanda ke shirin tsige Shugaban Majalisar, Alhaji Abdullahi Atta.

Tun a ranar Litinin ne dai, aka rufe majalisar inda wata majiya ta tabbatar da cewa jami'in da ke kula da sandar iko na majalisar ya boye sandar don ganin yunkurin tsige Shugaban majalisar bai samu nasara ba.

Gaskiya Kwankwaso Ya Yi Min Halacci, Inji Ganduje


Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce hakika tsohon Gwamna Sanata Rabi'u Kwankwaso ya taimake shi a shekarun da suka shafe suna siyasa tare.

Ganduje ya shaida wa majiyar mu ta BBC cewa sun shafe fiye da shekara 20 suna tafiyar siyasa tare da tsohon mai gidan nasa.

"Mun shafe shekaru muna siyasa tare... kuma ya taimake ni, ni ma na taimake shi, a zaman da muka yi," in ji Ganduje.

Manyan 'yan siyasar na Kano ba sa ga-maciji da juna tun bayan zaben shekarar 2015, inda tsohon Gwamnan na Kano Kwankwaso ya goyi bayan mataimakinsa Ganduje.

Bangaren Kwankwasiyya dai na zargin Ganduje da cin amanarsu da bita-da-kulli ta hanyar yin watsi da tsarin asalin gwamnatinsa.

Sai dai Gwamna Ganduje ya ce "a ganinmu ba a ci amanarsa ba sai idan shi ne bai fahimci abin da ake nufi da cin amana ba."

"Idan yana nufin cin amana shi ne, shi ya ba ni mulkin jihar Kano, ba Allah ba, to ina ganin wannan akidar da ya dauka haka ne."

Ya kara da cewa; "idan kuma ya dauka cewa ya taimake ni na zama gwamnan jihar Kano, amma kuma yana mun tadiya yadda gwamnati na ba za ta yi nasara ba, shi yake nufi da cin amana, to mu ba ma kallonsa a matsayin shi ne cin amana."

Da aka tambayi Ganduje kan dalilin da ya sa ya kori 'yan Kwankwasiyya daga gwamnatinsa, sai ya ce, "na yi watsi da su ne saboda yadda suka dinga yi wa gwamnat na zagon-kasa."

Ganduje ya ce "babu gwamnan da zai yarda ana ma sa zagon kasa a gwamnati, ko Kwankwaso ba zai yarda da haka ba."

Har ila yau Ganduje ya ce ba kamar yadda 'yan Kwankwasiyya ke nuna wa ba, shi kwararren dan siyasa ne.

"A ganinsu ba Allah ne yake ba da mulki ba, goyon bayansu ne, kuma ni a zaune kawai nake aka dauko ni aka ba ni, amma ni ma gogaggen dan siyasa ne," a cewar gwamnan, wanda ke shirin neman wa'adi na biyu.

'Ni ne kashin bayan jar hula'

Gwamnan ya ce babu yadda za a yi mutum ya haifi da, "daga baya kuma ya dawo ya ce zai dauki wuka ya yanka dan."

Rikicin Ganduje da Kwankwaso ya raba Jam'iyyar APC gida biyu a Kano, tsakanin bangaren da ke ganin yana takama da karfin gwamnati da kuma bangaren da ke ikirarin rinjayen goyon bayan jama'a.

Ganduje da magoya bayansa sun dage cewa babu wata illa da wannan rikici zai yi ga nasarar jam'iyyar a zabe mai zuwa, kuma za su iya lashe zabensu ba tare da wata matsala ba.

Sai dai wadansu masana na ganin akwai sake, inda suke cewa jam'iyyar APC za ta iya fuskantar babbar matsala matukar bangarorin biyu ba su shawo kan matsalolinsu ba.

*Rahoton BBC

Sunday 13 May 2018

AMBALIYAR RUWA A KANO: Gyara Kayanka Dai Ba Zai Zama Sauke Mu Raba Ba

DAGA ABBA ADAM ISAH

A madadin 'yan karamar hukumar Fagge matsabar Kwachiri muna kira da babbar murya akan a taimaka a fitar da mu wannan kangi da muke cikin na wannan aiki na alkairi da Dan majalisar jiha na kano da ya fara, amma yana nema ya zama aika-aika ga mazauna yankin. Saboda yadda ruwa ya yi ambaliya har cikin dakunan mutane, katifu da gadaje suna yawo saman ruwa. Hakan zai sa mazauna yankin su kasance cikin fargaba a duk lokacin da hadari ya hadu za a yi ruwa kai koda iska mai karfi ce ta kada sai hankulansu sun tashi saboda hali na ni 'ya su da suke tunanin za su shiga idan ruwan sama ya sauka.

Ya kamata dai idan dama an tsiri yin wannan aiki ne ya zama kwalli na kanfen 2019 to ga wata shawara a bi gidaje daya bayan daya a raba musu kwale-kwale domin tsallake ruwa idan gari ya waye domin siyo abun kari da kuma kai yara makaranta da fita harkokin yau da kullum saboda matasan yankunan ko zama da dogon wando ba sa yi saboda gudun kota kwanan ceton tsofaffi da kuma tsallakar da yara kanana daga gaba zuwa gaba.

Saturday 12 May 2018

Kotu Ta Tabbatar Da Gwamna M.A Abubakar A Matsayin Halastaccen Gwamnan Bauchi

Kotun koli ta tabbatar da Barista Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayin halataccen Gwamnan jihar Bauchi.

Idan ba a manta ba, Abdullahi Tanko Orlando ya gabatar da kara a gaban Kotu har ta kai ga Kotun koli na kalubalantar zaben fidda gwani da jam'iyyar APC ta yi a lokacin zaben fitar da gwani a 2015 wanda M.A ya yi nasara.

A yayin yanke hukunci a yau Juma'a Alkalin Kotun babban mai Shara'a, Mai Shari'a Utterle ya ce Tanko a karkashin doka ba shi da hurumin kalubalantar zaben fitar da gwani bayan an yi babban zabe.

Majiyar da cewa Shari'ar mai lamba ST/854/2015 ta kawo karshe a yau tare da tabbatar da Batista Mohammed Abdullahi Abubakar a matsayin Gwamna mai cikakken iko.

An Sauya Sunan Wani Asibiti A Kano Zuwa Sunan Isiyaka Rabi'u

Daga Anas Saminu Ja'en

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarin jihar Kano Malam Muhammad Garba ya sanyawa hannu, ya ce majalisar dokokin jihar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince da sakawa asibitin yara na Zoo suna zuwa Khalifa Sheikh Isyaku Rabi'u Pediatric Hospital.

Wannan abu ya yi daidai Allah Ta'ala ya gafartawa Malam ya kai rahama gare shi tare da magabatan mu baki daya.