Wednesday 16 May 2018

Gaskiya Kwankwaso Ya Yi Min Halacci, Inji Ganduje


Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce hakika tsohon Gwamna Sanata Rabi'u Kwankwaso ya taimake shi a shekarun da suka shafe suna siyasa tare.

Ganduje ya shaida wa majiyar mu ta BBC cewa sun shafe fiye da shekara 20 suna tafiyar siyasa tare da tsohon mai gidan nasa.

"Mun shafe shekaru muna siyasa tare... kuma ya taimake ni, ni ma na taimake shi, a zaman da muka yi," in ji Ganduje.

Manyan 'yan siyasar na Kano ba sa ga-maciji da juna tun bayan zaben shekarar 2015, inda tsohon Gwamnan na Kano Kwankwaso ya goyi bayan mataimakinsa Ganduje.

Bangaren Kwankwasiyya dai na zargin Ganduje da cin amanarsu da bita-da-kulli ta hanyar yin watsi da tsarin asalin gwamnatinsa.

Sai dai Gwamna Ganduje ya ce "a ganinmu ba a ci amanarsa ba sai idan shi ne bai fahimci abin da ake nufi da cin amana ba."

"Idan yana nufin cin amana shi ne, shi ya ba ni mulkin jihar Kano, ba Allah ba, to ina ganin wannan akidar da ya dauka haka ne."

Ya kara da cewa; "idan kuma ya dauka cewa ya taimake ni na zama gwamnan jihar Kano, amma kuma yana mun tadiya yadda gwamnati na ba za ta yi nasara ba, shi yake nufi da cin amana, to mu ba ma kallonsa a matsayin shi ne cin amana."

Da aka tambayi Ganduje kan dalilin da ya sa ya kori 'yan Kwankwasiyya daga gwamnatinsa, sai ya ce, "na yi watsi da su ne saboda yadda suka dinga yi wa gwamnat na zagon-kasa."

Ganduje ya ce "babu gwamnan da zai yarda ana ma sa zagon kasa a gwamnati, ko Kwankwaso ba zai yarda da haka ba."

Har ila yau Ganduje ya ce ba kamar yadda 'yan Kwankwasiyya ke nuna wa ba, shi kwararren dan siyasa ne.

"A ganinsu ba Allah ne yake ba da mulki ba, goyon bayansu ne, kuma ni a zaune kawai nake aka dauko ni aka ba ni, amma ni ma gogaggen dan siyasa ne," a cewar gwamnan, wanda ke shirin neman wa'adi na biyu.

'Ni ne kashin bayan jar hula'

Gwamnan ya ce babu yadda za a yi mutum ya haifi da, "daga baya kuma ya dawo ya ce zai dauki wuka ya yanka dan."

Rikicin Ganduje da Kwankwaso ya raba Jam'iyyar APC gida biyu a Kano, tsakanin bangaren da ke ganin yana takama da karfin gwamnati da kuma bangaren da ke ikirarin rinjayen goyon bayan jama'a.

Ganduje da magoya bayansa sun dage cewa babu wata illa da wannan rikici zai yi ga nasarar jam'iyyar a zabe mai zuwa, kuma za su iya lashe zabensu ba tare da wata matsala ba.

Sai dai wadansu masana na ganin akwai sake, inda suke cewa jam'iyyar APC za ta iya fuskantar babbar matsala matukar bangarorin biyu ba su shawo kan matsalolinsu ba.

*Rahoton BBC

No comments:

Post a Comment