Friday 4 May 2018

KANO: Daliban jami’ar kimiyya ta Wudil sun yi zanga zanga kan mutuwar wani dalibi

Daliban jami’ar kimiyya da fasa ta Wudil a jihar Kano sun yi zanga zanga a harabar Makarantar domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda wani dalibi ya rasu a ruwan wudil.

Lamarin dai ya auku ne a lokacin da wasu dalibai su uku, sun je wanka a cikin kogin Wudil ne, inda suka nitse a ruwa, biyu daga cikinsu sun ci nasarar tsira da ransu, yayin da daya dalibin mai suna Farouk Abubakar dan aji uku ya nitse.

A lokacin da lamarin ya auku daliban sun yi gaggawar kai labarin zuwa makaranta, inda aka nemi Sarkin Ruwa na garin Wudil da misalin karfe 6:30na yamma domin samu a ceto rayuwar dalibin, shi kuma yace sam basa shiga ruwa idan duhu yayi.

A wannan yanayi ne dalibin Farouk Abubakar ya rasu, Farouk dalibi ne dake karantar kimiyyar tsirrai a aji na uku, kafin Allah yayi masa cikawa a ranar Laraba.

Daliban dai sun tare hanyar da ta hada Wudil zuwa Gaya, inda suka yi ta kone kone da fashe fashe akan hanya, Shugaban makarantar Shehu Alhaji, ya ja hankalin daliban da su zauna lafiya, a lokacin da ya ziyarci gabar ruwan inda aka ciro gawar dalibin bayan ya rasu.

Haka kuma, Shugaban makarantar ya bayar da hutun ranakunn Alhamis da Juma’a domin nuna alhinin rasuwar dalibin.

No comments:

Post a Comment