Wednesday 16 May 2018

Malaman Darika Sun Dace Da Mabiya, Sai Dai Mabiyan Ne Ba Su Dace Da Malamai Ba, Inji Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum

An bayyana cewar a fili yake Shehunnan Darika sun dace da mabiya masu tsananin biyayya a gare su ido rufe, amma su mabiyan ne ba su mori Malamai wadanda za su dora su akan tafarki mikakke na Sunnar Annabi Muhammadu SAW ba, wanda hakan ne dalilin jefa mabiyansu cikin dimuwa da fagamniya a rayuwarsu.

Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah Wa Ikamatus Sunnah na kasa baki daya Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachikum ya bayyana hakan, a yayin da yake tsokaci dangane da ikirarin da 'Yan Darika suka yi na cewar wai sun ga Shehun su Ibrahim Nyass karara a jikin fitilar haska Titi a yayin gudanar da mauludin da sukayi na Shehun a Abuja, a wata tattaunawar da yayi da manema labarai a gidan shi dake Rigachikum Kaduna.

Sheikh Sambo Rigachikum ya cigaba da cewar, ko shakka babu tsananin makauniyar biyayya da kauna ido rufe da 'Yan Darika ke yiwa Shehunnan su ya sanya suka amince da wannan magana, amma maimakon Malaman nasu su fito fili su gaya musu gaskiya, sai suka kara burma su, suka tabbatar musu da cewar lallai Shehu Nyass aka gani cikin fitila, sannan kuma ana ganin shi a wurare daban daban kamar a jikin bango ko a bayan daki ko kuma a jikin madubi da sauran wasu wurare, wanda su kansu Malaman da ke fadin haka sun san ba gaskiya suke fada ba, amma saboda wasu dalilai na son zuciya sai su kayi amfani da jahilcin mabiyan su suka kara kifar da su, " Ai idan akwai wanda ya dace ace ana gani bayan rasuwarshi to Annabi Muhammadu ne, amma babu inda akaji labarin cewar Sahabbai ko Tabi'ai sun ganshi bayan rasuwar shi, a bisa ga wannan da akwai damuwa kwarai da gaske da yadda Malaman Darika ke cutar da mabiyan su ta hanyar cewa ana ganin wani Mahaluki bayan mutuwar shi, idan da ace Malaman Darika za su mayar da hankali wajen karantar da mabiyan su addini yadda yake to wallahi da an samu kyakkyawan cigaba, duba da irin biyayyar da sukeyi wa Malaman nasu, akan haka nake kara jaddada cewar Shehunnan Darika sun dace da mabiya, Mabiyan ne basu dace da Malamai ba " Inji shi.

Dangane da batun Watan Ramadan da za'a shiga ciki kuwa, babban Malamin yayi kira ga Jama'ar Musulmi da su kara gyara halayen su gami da tuba zuwa ga Ubangiji, sannan su kyautata mu'amulolin su da juna, 'Yan kasuwa suji tsoron Allah kada su tsawwala farashin kayayyaki,  sannan Malamai masu Tafsirai su gudanar da Tafsiran su akan tsari da karantarwar sunnar Annabi, a kauce wa dukkanin wani yarfe da huce haushi akan wani, domin Munbarin tafsiri ba fage na banbadanci da tumasanci ba, waje ne na ilimantar da Al'umma Addinin Musulunci.

Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachikum ya kuma yi Addu'a ga Jihar Kaduna da kasa Nijeriya gaba daya na Allah ya zaunar da kasar lafiya, dukkanin fitintinu dake addabar kasar Allah ya kawo saukin su, Allah ya sa mu dace da alkhairan dake cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan, sannan yayi Addu'ar Allah ya Jikan Malamai magabata wadanda suka rigamu gidan gaskiya, kamar su Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Ismail Zakariyya Jos da Sheikh Jafar Mahmud Adam da sauran Al'ummar Musulmi gaba daya.

No comments:

Post a Comment